Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Chelsea da Man United sun raba maki a tsakaninsu a Premier
Chelsea da Manchester United sun tashi 1-1 a wasan mako na 13 a gasar Premier da suka kara ranar Asabar a Stamford Bridge.
Kungiyoyin biyu sun tashi wasa ba ci a minti na 45, daga nan suka je hutu, sannan suka koma zagaye na biyu.
Saura minti uku lokaci ya cika Chelsea ta ci kwallo ta hannun Jorginho a bugun fenariti.
Cikin 'yan wasan da suka ci kwallo 20 ko fiye da haka a Premier League, Jorginho ya ci fenariti 19 daga 21 da ya ci a babbar gasar tamaula ta Ingila.
Daga baya ne sabon dan wasan da United ta dauka a bana daga Real Madrid, Casemiro ya farke.
Wasa na 26 a Premier League da suka yi canjaras tsakanin Chelsea da Manchester United kenan.
Ciki har da karawa tara baya, bakwai daga ciki canjaras suka yi da biyar a jere.
Da wannan sakamakon Chelsea tana mataki na hudu a teburin Premier da maki 21 da tazarar maki daya tsakaninta da United ta biyar.
Wasan da suka buga a bara:
2021/2022
Premier League Alhamis 28 ga watan Afirilun 2022
- Man Utd 1 - 1 Chelsea
Premier League Lahadi 28 ga watan Nuwambar 2021
- Chelsea 1 - 1 Man Utd
Wasu batutuwa da suka shafi wasan Chelsea da Manchester United kafin karawar Asabar:
Chelsea ta kara da United wasa tara baya ba tare da cin kungiyar Old Traffors ba da yin canjaras shida da rashin nasara uku.
Cikin wasa shida da United ta ziyarci Chelse a karawar baya ta ci uku da canjaras uku, kenan ba a doke ta ba.
Kungiyoyin nan sun yi canjaras 25 tsakanin Chelsea da Manchester, shi ne kan gaba da aka yi canjaras da dama.
Chelsea
Tun bayan da Graham Potter ya karbi aikin horar da Chelsea, kungiyar ta yi wasa bakwai da cin biyar da canajaras biyu.
Haka kuma kungiyar ta yi karawa takwas ba a doke ta ba a gida har da yin nasara a wasa uku a jere a Stamford Bridge.
Chelsea ta yi karawa uku a jere ba tare da kwallo ya shiga ragarta ba, kafin nan sai da ta buga fafatawa shida ana zura mata kwallaye a raga.
Graham Potter - ya ci United 2-1 a Old Trafford cikin Agusta lokacin yana Brighton.
Yana fatan zama na farko da zai doke United karo na biyu a jere a kungiya Chelsea, bayan wanda ya yi a Brighton.
Mai rike da wannan bajintar shi ne Andy Aitken wanda ya yi nasara a kan United wasa biyu, dayan a Middlesbrough da kuma a Leicester City a kakar1908-09.
Cesar Azpilicueta na fatan yin kan-kan-kan da tsohon mai tsaron raga, Petr Cech wanda ya tsare ragar Chelsea sau 333 a Premier League.
Manchester United
Manchester United ta ci wasa uku daga hudun da ta yi a waje a Premier League da rashin nasara daya.
An zura kwallo a ragar United a kalla hudu daga biyar a wasa 11 da ta fafata a waje.
Marcus Rashford ya ci Chelsea kwallo biyar da bayar da biyu aka zura a raga a dukkan karawar da ya fuskanci kungiyar.
Rashford na bukatar cin kwallo biyu su zama 100 da ya ci wa United a dukkan fafatawar da ya yi mata.
United ta buga wasa biyu a waje da wadanda ke na farko zuwa tsakiyar teburin Premier, inda ta sha kashi 4-0 a hannun Brentford da 6-3 a hannun Manchster City.
United ta yi rasahin nasara a wasa uku a jere a birbin Landan, mafi mufi kenan tun biyar da ta yi tsakanin Afirilun 1973 zuwa Janairun 1974.