Malafa da dawakai a cikin hotunan Afirka na mako 14-20 ga Oktoban 2022

An wallafa

Ga wasu zaɓɓɓun hotuna na wasu abubuwan da suka faru a nahiyar Afira ko na wasu ƴan Afirka a wasu sassan duniya a makon da ya gabata.

Big smiles on Friday at a camp for refugees from Western Sahara in Tindouf, south-west Algeria.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Murmushi da farin ciki a sansanin ƴan gudun hijira da ke Yammacin Sahara a kudu maso yammacin Aljeriya a ranar Juma'a.
More smiles from Nigeria's Chikamso Jiwuaku during a training session ahead of their Fifa U-17 Women's World Cup 2022 Group B match against Chile on Monday. The Flamingos' 2-1 win sees them qualify for the quarter-finals of the competition.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Ƙarin murmushi daga fuskar ƴar Najeriya Chikamso Jiwuaku a lokacin wani atisaye gabanin wasan da ƙasar ta fafata da Chile a Gasar Cin Kofin Duniya ta mata ta ƴan ƙasa da shekara 17 a ranar Litinin.
On Monday, a Maasai woman waits to buy hay for her cows affected by worsening drought in parts of East Africa...

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, A ranar Litinin aka ɗauki hoton wannan matar ƴar ƙabilar Maasai wacce ta je sayen abincin shanunta da matsalar fari ke shafa a wasu sassan gabashin Afirka...
She is at a temporary animal feed market in the Ilbisil settlement of Kajiado, Kenya, where cows have become emaciated.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Ta je kasuwar abincin dabbobi ta Ilbisil da ke Kajiado a Kenya, inda dabbobi suke yayyanƙwane.
Shops are locked in Ghana on Wednesday because traders in Accra are protesting against the country's worsening economic conditions.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, An rufe shaguna a Ghana ranar Laraba saboda ƴan kasuwa na nuna fushinsu kan taɓarɓarewar yanayin tattalin arziki a ƙasar.
Women harvest tomatoes in Mondoukou, on the outskirts of Abidjan, Ivory Coast, a day before the International Day of Rural Women...

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Mata na girbe tumatur a Mondoukou a wajen birnin Abidjan na ƙsar Ivory Coast, kwana ɗaya kafin bikin Ranar Matan Karkara ta Duniya...
The day highlights the role and situation of women in rural areas, and Dibang women are out celebrating on Saturday in Cameroon...

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Ana bikin ranar ne don yin duba kan halin da mata ke ciki a ƙauyuka, kuma matan ƙauyen Dibang sun yi bikin ranar a ran Asabar a Kamaru...
Where another group of women also dance on the road. The International Day was established by the United Nations and first observed in 2008.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Wasu matan kuma raye-raye da kaɗe-kaɗe suka tsara yi a ranar. Majalisar Ɗinkin Duniya ce ta ƙirƙiri ranar a shekarar 2008.
A boy enjoys the community kite-flying in South Africa on Wednesday during the Cape Town International Kite Festival.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Wani yaro yana wasa da jirgin leda a wajen bikin wasan jirgin leda na ƙasa da ƙasa a ranar Laraba a birnin Cape Town na Afirka ta Kudu.
Femi Kuti (L), son of Nigerian Afrobeat legend Fela Anikulapo-Kuti, performs on stage with his son Made Kuti during the annual concert in honour of their father and grandfather in Lagos, on Sunday.

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Femi Kuti daga hagu ɗan fitaccen mawaƙin Afro na Najeriya marigayi Fela Anikulapo-Kuti, yana wasa tare da ɗansa Made Kuti a wani taro na tunawa da mahaifinsa a Lagos ranar Lahadi.
Breeder Moeketsi Maieane and his two-year-old Basotho pony, Morumua Hana Lonya, pose outside his house in Lesotho...

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, An ɗauki hoton wannan mai kiwon Moeketsi Maieane da dokinsa mai shekara biyu Basotho pony, a wajen gidansa a Lesotho...
A day before competing in a traditional race in Semonkong, a remote town in the Maluti mountains...

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Kwana guda kafin nan ya kasance a cikin gasar tseren dawaki da daka yi a Semonkong da ke wajen tsaunuka...
These herders meet at a local tavern before heading to the competition on Saturday.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Waɗannan makiyayan sun hadu a wani waje kafin gasar a ranar Asabar.
A policeman fires towards protesters in Ettadhamen, a working-class suburb in the Tunisian capital on Friday...

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Wani ɗan sanda yana harbi a kan masu zanga-zanga a Ettadhamen, wata unguwa ta ma'aikata a babban birnin Tunusiya a ranar Juma'a...
After protesters clash with police following the death of 24-year-old Malek Sellimi who was injured during a police chase last month.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Masu zanga-zanga sun yi faɗa da ƴan sanda sakamakon mutuwar wani matashi Malek Sellimi mai shekara 24, wanda ƴan sanda suka yi wa rauni a watan da ya gabata.
On Sunday, people take shelter during a hailstorm in Windhoek, Namibia.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Wannan hoton an ɗauke shi ranar Lahadi a yayin da mutane suke samun mafaka daga ruwan sama a birnin Windhoek na Namibia.
On the same day, spectators are thrilled by a display at the International Aerospace and Defence Exhibition in Sousse, Tunisia.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, A wannan ranar kuma aka yi wannan hoton na wasu mutane suna kallon shawagin jiragen sama a Sousse da ke Tunisia.
A motorcyclist enjoys a fresh fruit juice in the Gamaliya district of Egyptian capital, Cairo, on Saturday.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Wani mai abbur yana shan lemon kayan marmari a gundumar Gamaliya da ke Alkahira babban birnin MAsar a ranar Asabar.
The sun sets over the Mediterranean Sea in Libya, where a fisherman bides his time on Tripoli's waterfront on Monday.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Wani mai kamun kifin a bakin aiki a lokacin da rana ke shirin faɗuwa a gaɓar tekun Bahar Rum da ke Libiya ranar Litinin.