Real Madrid ta kasa karbar teburin La Liga a gun Girona

Asalin hoton, Getty Images
Real Madrid ta kasa komawa ta daya a teburin La Liga, bayan tashi 0-0 da Rayo Vallecano a wasan mako na 12 a La Liga ranar Lahadi a Santiago Bernabeu.
Rabon da Rayo ta tashi ba ci a gidan Real Madrid a babbar gasar tamaula ta Sifaniya tun ranar 29 ga watan Maris din 2000, kenan shekara 23 da ta wuce.
Real wadda ta yi fatan komawa matakin farko a teburin La Liga ta ci gaba da zama ta biyu da maki 29.
Giron, wadda ta je ta ci Osasuna 4-2 ranar Asabar ta koma jan ragamar teburin La Liga mai maki 31.
Barcelona ce ta uku da tazarar maki biyu tsakaninta da Real Madrid a babbar gasar tamaula ta Sifaniya.
Ita kuwa Rayo mai maki 18 tana ta tara a kan teburin babbar gasar tamaula ta Sifaniya.
Wasan La Liga da suka kara a bara:
Sifanish La Liga Laraba 24 ga watan Mayun 2023
- Real Madrid 2 - 1 R. Vallecano
Sifanish La Liga Litinin 7 ga watan Nuwambar 2022
- R. Vallecano 3 - 2 Real Madrid
'Yan wasan da Real ta fuskanci Rayo da su:
'Yan wasan Real Madrid:
Masu tsaron raga: Lunin, Kepa da kuma Diego Piñeiro.
Masu tsaron baya: Carvajal, Alaba, Nacho, Lucas V., Fran García da kuma Rüdiger.
Masu buga tsakiya: Bellingham, Kroos, Modrić, Camavinga, Valverde, Arda Güler da kuma Nico Paz.
Masu cin kwallaye: Vini Jr., Rodrygo, Joselu da kuma Brahim.
Wasannin da za a buga ranar Lahadi:
- Deportivo Alaves 1-0 Almeria
- Valencia 1-0 Granada
- Villarreal 2-3 Athletic Bilbao
- Real Madrid 0-0 Rayo Vallecano










