Marseille ta kusan ɗaukar Hojbjerg daga Tottenham kan £17m

Asalin hoton, Getty Images
Ƙungiyar da ke buga Ligue 1, Marseille ta yi nisa kan tattaunawa da Tottenham, domin sayen ɗan ƙwallon tawagar Denmark, Pierre-Emile Hojbjerg.
Ana cewa mai shekar 28 na son barin Arewacin Landan, wanda aka yi hasashen cewar darajarsa ta kai kimanin £17m.
Yanzu ya rage kan yadda za a biya ƙudin cinikin ɗan wasan, amma dukkan ƙungiyoyin sun amince da su kulla yarjejeniya a tsakaninsu.
Hojbjerg ya koma Tottenham a 2020 kan £15m daga Southampton a lokacin da Jose Mourinho ke jan ragama.
Ya buga wasa 39 a bara, wanda aka fara 10 da shi a cikin fili, bayan da sabon koci, Ange Postecoglou ke amfani da Yves Bissouma da Pape Matar Sarr a tsakiyar fili.
Ɗan wasan ya shiga yarjejeniyar karshe a Tottenham, wadda za ta kare a karshen kakar 2024/25.
Tottenham tana ta kokarin kara karfin gurbin masu buga mata tsakiya, inda ta ɗauki Archie Gray daga Leeds da kuma Lucas Bergvall daga Djurgardens ta Sweden.
Marseille na cin gaba da yin cefane don taka rawar gani a kakar da za a shiga, wadda ta nada tsohon kociyan Brighton, Roberto de Zerbi a matakin mai horar da ita.
Tuni kuma kungiyar da ke buga Ligue 1 ta ɗauki Mason Greenwood daga Manchester United da Ismael Kone daga Watford a watan nan, sannan an ce tana son taya ɗan wasan Arsenal, Eddie Nketiah.










