Arteta ya ɗauki laifi kan rashin nasarar Arsenal

Mikel Arteta

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Kocin Arsenal Mikel Arteta ya bayyana rashin jin daɗin sa bayan da aka fitar da ƙungiyarsa daga gasar cin kofin Carabao a zagaye na huɗu bayan da West Ham ta doke su da ci 3-1.

Arteta ya yi canje-canje shida na 'yan wasan da suka fara karawar da ƙungiyar ta yi da Sheffield United a gasar Premier, inda ya ajiye Declan Rice da Bukayo Saka da kuma kyaftin Martin Odegaard a benci.

'Yan wasan da suka fara wasan ba su taka rawar gani ba, kuma Arteta ya amsa laifin.

"Na ji takaicin yadda wasan ya kasance, amma laifi na ne," in ji shi.

''Ba haka muka so mu buga wasan ba, kuma ba mu sami damar yin hakan ba. Akwai baƙin ciki duk lokacin da muka yi rashin nasara''.

Duk da cewa Rice da Odegaard da Saka sun shiga wasan daga baya, ba su iya hana Arsenal shan kashi a wasan ba.

Arsenal za ta fafata da Newcastle United a wasanta na gaba a gasar Premier ranar Asabar mai zuwa.