Tagwaye manne da juna da aka fitar da ran za su rayu na bai wa duniya mamaki

An wallafa

Ba a yi tsammanin Marieme da Ndeye za su iya rayuwa fiye da 'yan kwanaki ba bayan da aka haife su.

A yanzu da suka kai shekara bakwai, ana tunanin su ne kaɗai tagwayen da ke manne da juna a Turai.

Duk da cewa yaran biyu suna da halaye da yanayi daban-daban, suna dogara kan junan su domin rayuwa.

"Idan aka faɗa maka da farko cewa babu makoma, kawai kana rayuwa ne domin yanzu," in ji mahaifinsu, Ibrahima.

Ba kasafai aka cika samun 'yan biyun da ke haɗe da juna ba - kusan ɗaya cikin duk haihuwa dubu ɗari biyar a Birtaniya.

Kusan rabi ba sa zuwa a raye yayin sannan kashi ɗaya bisa uku na mutuwa cikin sa'a 24 bayan haihuwarsu.

Don haka ganin Marieme da Ndeye na bikin cika shekara bakwai tare da ƙawaye, ba wai kawai yana faranta ran Ibrahima ba kaɗai, har da suma likitocin da ke kula da su.

Marieme da Ndeye na da ƙafa biyu da ƙugu ɗaya amma kowacce a cikinsu tana da ƙashin baya da kuma zuciya.

Suna samun kula a kowane lokaci amma suna zuwa makaranta a South Wales tare da ƙawayensu.

"Yayana sun banbanta. Marieme ba ta da magana, ba ta son shiga mutane, amma ya sha banban da halayyar Ndeye wadda ba ta dogara a kan mutane.

"Ba zan yi ƙarya ba cewa da sauƙi amma dama ce babba. Kana jin wata nasara ganin yadda suke fafutukar rayuwa."

Lokacin da aka haifi tagwayen a Senegal a 2016, iyayensu sun yi tunanin jariri ɗaya za su haifa. Likitoci ba su yi tsammanin za su rayuwa mai tsawo da ta wuce ta 'yan kwanaki ba.

"Na soma shirin rasa su ma," kamar yadda Ibrahima ya shaida wa BBC a shirin labarin 'yan uwan junan da ba sa rabuwa

"Abin da kawai muke iya yi shi ne mu kasance tare da su sannan ka da mu yi nesa da su. Mun gani ƙarara da farko-farko cewa muna tare da jarumai, waɗanda ke da ƙwarin rai."

Ana tunanin raba su ne kaɗai hanyar da za ta sa su rayu, a cewar likitoci a Senegal.

Bayan kiran asibitoci a sassan duniya ana neman taimako, iyalan sun isa Birtaniya domin kula da tagwayen a asibitin Great Ormond Street da ke London a 2017.

Ibrahima ya yi fatan cewa fitaccen asibitin yaran, wanda ya taɓa 'yan biyun da ke manne da juna da dama fiye da ko ina a duniya, zai iya raba su sannan za su iya koma wa gida ga 'yan uwansu a Dakar amma hakan ba ta faru ba.

An gudanar da gwaje-gwaje da suka gano zuciyar Marieme na da rauni a gudanar da tiyatar kuma ba za ta rayu bayan tiyatar ba.

Ibrahima da tawagar ƙwararrun likitocin sun yi magana mai tsawo kan ko a raba su ko kuma a ƙyale yaran.

Daga bisani an yanke shawarar a ƙyale su manne da juna.

A lokacin Ibrahima ya ce "kamar kashe ɗaya daga cikin 'ya'yana ne, abu ne da ba zan iya ba."

"Ba zan iya bari na zaɓi wanda zai rayu ko wanda zai mutu ba yanzu."

Yayin da mahaifiyarsu ta koma Afirka domin kula da sauran yaransu, Marieme, Ndeye da Ibrahima sun ci gaba da zama a Birtaniya domin kulawar likitoci sannan su ukun suka wuce zuwa Cardiff.

Wani labarin ƙ arfafa gwiwa na rayuwar tagwaye manne da juna 'yan shekara bakwai waɗanda ba a yi tsammanin za su yi rayuwa mai tsawo ba.

"Rashin iya komawa gida abu ne mai matuƙar wahala saboda akwai sauran iyalinka, ga kuma aikinka a can gida," a cewar Ibrahima wanda shi ne tsohon daraktan gudanarwa na wani kamfanin tafiye-tafiye a Senegal.

"Kamar mace ce mai ciki amma ban jefa kaina cikin tunani ba, kawai na bi zuciyata ne. Nauyina ne a matsayin uba na tabbatar suna da wanda ke tare da su."

Tagwayen na buƙatar zuwa asibiti a kai a kai saboda suna cikin babban haɗarin kamuwa da cuta da kuma tsayawar bugun zuciya.

"Da farko, abu ne na murna daga baya kuma ka gano cewa wannan abu ne da kwai na karanta a litattafai," in ji Dakta Gillian Body, wani likitan yara a asibitin jami'ar Wales.

"Suna da ƙafafu biyu da ƙugu ɗaya. Sannan a cikinsu, akwai gaɓoɓi daban-daban. Ba mu san daidai ina ba amma mun san suna amfani da wasu tare sannan suna da wasu daban-daban.

"Kowacce tana da ƙashin baya haɗe da jijiyoyi kuma gaba ɗaya sun iya tafiyar da lamarinsu sannan ba sai sun faɗa wa junan su yadda za su miƙar da hannu ko yadda za su matsar da ƙafa ba, kawai suna yi."

"Dole ka sayi riga iri biyu sannan ka kai wajen tela a haɗe su," in ji Ibrahima.

"Suna da ƙafa biyu don su samu wanduna amma kwankwasonsu yana da faɗi, toh dole ka kai shago a gyaggyara musu."

Iyalin a yanzu sun haɗe da al'ummar yankin Cardiff kuma tagwayen suna samun kula dare da rana yayin da masu basu kulawa ke tallafa wa mahaifinsu.

Suna aji uku a makarantar firamaren da suke zuwa inda ma'aikata ke kula da su.

"Ina son su yi rayuwa kamar kowa, su yi wasa su yi dariya da yara su kuma yi ƙawaye, su girma," in ji Ibrahima.

"Ba sai sun ɓoye kansu ba kuma kasancewarsu a makaranta ya nuna suna cikin al'umma kuma sun yi nasarar kasancewa wani ɓangare na wannan al'umma."

Ƙalubale na gaba ga Marieme da Ndeye shi ne su fara ƙoƙarin tsayawa da tafiya. A yanzu suna iya tashi tsawon kimanin minti ashirin duk rana amma da taimakon abin tsayawa.

"Sun cimma abubuwa da dama da ba a yi tunanin za su iya ba," kamar yadda Ibrahima ya ce.

"Idan aka faɗa maka daga farko cewa babu makoma, kana rayuwa ne domin yanzu," ya ƙara da cewa.

"Na san cewa a kowane lokaci, ina iya samun kiran waya cewa wani abu mara daɗi ya faru.

"Tsawon yaushe? Ba na son sani. Muna son kowace rana ta zama ta ban mamaki tare da murnar rayuwa.

"Abu ne da ka iya zuwa da saɓani amma kana samun nasara duk da irin ƙalubalen da kake ciki. Suna sani farin ciki. Babbar baiwa ce kasancewa ta mahaifinsu."