Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Na karɓi saƙon salula da ya ƙara min ƙwarin gwiwa - Pochettino
Mauricio Pochettino ya ce ya samu saƙon salula daga mahukuntan Chelsea a lokacin da yake fuskantar kora, bayan da aka doke shi karo biyu a jere.
Hakan ya sa Chelsea ta yi kasa zuwa mataki na 11 a teburin Premier League, bayan da Wolverhampton ta ci Chelsea 4-2 a Stamford Bridge ranar Lahadi.
Chelsea ta kashe sama da fam biliyan daya wajen sayen sabbin ƴan wasa tun bayan da Todd Boehly ya sayi kungiyar a cikin Mayun 2022.
To sai dai wasa tara Pochettino ya yi nasara a Premier League ta bana, wadda aka buga karawa 23 kawo yanzu.
Matsi ya fara hawa kan kociyan ɗan kasar Argentina, bayan da Liverpool ta ci Chelsea 4-1, kwana hudu tsakani Wolves ta kara ɗura mata 4-2.
Kungiyar Chelsea wadda take ta 11 a teburi tana da tazarar maki 15 tsakanin ta da gurbin ƴan hudun farko da tazarar maki biyar tsakaninta da abokiyar hamayyarta West Ham United, wadda take ta bakwai.
Duk da makudan kudin da Boehly ya kashe na sayen Chelsea daga Roman Abramovich, amma ta kare a gurbi mafi muni wato na 12 a teburin Premier a bara.
Bayan da magoya baya suka yi masa ihu a Stamford Bridge ranar Lahadi, bayan tashi wasa da Wolves, Pochettino ya bukaci hadin kai daga magoya bayan kungiyar.
Chelsea za ta ziyarci Aston Villa ranar Laraba, domin buga wasa na biyu a zagaye na hudu a FA Cup.
Chelsea ta kai zagayen karshe a Carabao Cup da za ta fuskanci Liverpool nan gaba a Wembley.