Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Kovacs ne zai busa wasan Liverpool da Real Madrid
Liverpool za ta karbi bakuncin Real Madrid ranar Talata a wasan farko a zagayen 'yan 16 a Champions League a Anfield.
Tuni aka nada alkalin wasa, Istvan Kovacs, wanda zai hura karawar ta hamayya a Ingila.
Wannan shine karo na biyu da zai hura wasan Real Madrid a Champions League, bayan fafatawar da kungiyar Sifaniya ta doke Manchester City 4-3 a bara.
Mai shekara 38 ya fara alkalanci a gasar tamaula ta Romania a 2007 daga nan ya zama raflin Fifa a 2010.
Liverpool, wadda ta ci Newcastle 2-0 ranar Asabar a Premier League karawar mako na 24 tana ta tara a teburi da maki 35.
Real Madrid kuwa ta doke Osasuna 2-0 ranar Asabar a mako na 22 a La Liga, tana ta biyu a teburi mai maki 51.
Real Madrid ta doke Liverpool 1-0 ta lashe Champions League na 14 jimilla a Faransa a bara.
Wannan shi ne wasa na 10 da za a kece raini tsakanin kungiyoyin biyu, inda Liverpool ta ci uku da canjaras daya, Real ta yi nasara a biyar.