Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Dan wasan Portugal Neto ba zai buga World Cup ba
Kungiyar kwallon kafa ta Wolves tace dan wasan gabanta ba zai buga gasar cin kofin duniya mai zuwa da za a yi a Qatar saboda za a yi masa aiki a idon hawunsa.
Dan wasan mai shekara 22 ya ji rauni ne a wasan da suka sha kashi da ci 2-0 a hannun West Ham a ranar Asabar din da ta gabata, aka yi kuma canjin shi a minti 24 da fara wasan.
Kungiyar ta Premier ta ce Neto ya ji raunin ne a mahadar kan idon sawunsa.
"Bayan kara ganin kwararrun lafiya da kuma jin ra'ayinsu a wannan makon, an gama tsara cewa za a yi masa tiyata," kamar yadda sanarwar da kungiyar ta fitar ta bayyana.
"Wannan na nufin ya yi rashin sa a, ba zai zama ya warke tsaf ba kafin fara World Cup."
Neto ya buga wa Portugal wasa uku a wannan kakar, ya kuma kasance cikin tawagarsu da ta buga wasan Nations League da Czech Republic da Spain, amma bai buga ko daya ba.
Za a fara gasar cin kofin duniyar ne daga 20 ga watan Nuwambar zuwa 18 ga watan Disamba a Qatar.