Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yannick ya koma Barca, bayan da kwantiraginsa ya kare a AC Milan
Barcelona ta cimma yarjejeniyar daukar Franck Yannick Kessier, wanda kwantiraginsa ya kare a AC Milan a watan jiya.
Dan wasan zai sa hannu kan yarjejeniyar da za ta kare ranar 30 ga watan Yunin 2026.
Haka kuma Barcelona ta sa farashin yuro miliyan 500 ga duk kungiyar da ke son daukar dan wasan, idan yarjejeniyarsa ba ta kare ba a Camp Nou.
Ranar Laraba 6 ga watan Yuli, Barcelona za ta gabatar da Franck Yannick Kessie a matakin dan wasanta.
An haifi Franck Kessie ranar 19 ga watan Disambar 1996 a garin Ouragahio da ke Ivory Coast.
Mai taka leda daga tsakiya ko tsaron baya daga tsakiya ya fara tamaula a Stella Club d'Adjame ta Ivory Coast daga baya ya koma Atalanta a 2014.
Bayan da ya taka rawar gani a kakar 2016/17 a Atalanta, daga nan ne AC Milan ta yi zawarcin dan kwallo.
Dan wasan ya koma Milan buga wasannin aro a 2017 daga nan ta saye shi a 2019 kan yuro miliyan 33.
Kaka biyar da Kessie ya yi a Milan ya kara samun gogewa, ya kuma ci kwallaye, ya kuma bayar an zura a raga.
Dan wasan tawagar Ivory Coast ya taimakawa Milan ta dauki Serie A a kakar da aka Karkare, kofin farko da ta dauka tun bayan kaka 11..