Chelsea ta ƙara yin tuntuɓe a Stamford Bridge

An wallafa

Brentford ta je ta doke Chelsea da ci 2-0 a wasan mako na 10 a gasarr Premier League da suka buga ranar Asabar a Stamford Bridge.

Wasa na uku kenan da Brentford ta yi nasara a bana, inda Ethan Pinnock da Bryan Mbeumo suka ci mata kwallayen.

Chelsea, wadda ta ɓarar da damar maki da yawa an zura mata kwallon farko da ka ta hannun Pinnock, bayan da ya samu tamaula daga Mbeumo.

Kwallo ta biyu kuwa kwana za a kwaso zuwa gidan Brentford, inda golan Chelsea, Robert Sanchez ya je ko zai samu nashi rabon.

Daga nan kwallon ya je wajen Neal Maupay na Brentford, wanda ya ja zuwa ragar Chelsea, sannan ya bai wa Mbeumo ya zura a raga.

Karo na uku a jere da Brentford ta je Stamford Bridge ta ci Chelsea a Premier League.

Haka kuma wasa na huɗu kenan da Chelsea ta kasa nasara a kan Brentford, wadda ta yi nasara uku da canjaras ɗaya, sannan ta ci kwallo shida aka zura mata ɗaya a raga.

Tun kan wannan karawar, wasa biyu Chelsea ta yi nasara daga 12 na hamayya da ƙungiyoyin Landan, wadda aka doke a wasa shida da canjaras huɗu.

Ƙungiyoyin da suka ci Chelsea a bana a Premier League sun haɗa da Nottingham Forest da Aston Villa da kuma Brentford.

Da wannan sakamakon Brentford ta koma ta 10 a kan teburi kafin sauran ƙungiyoyi su buga wasannin mako na 10 ranar Asabar da Lahadi.

Ranar Laraba, Chelsea za ta karɓi bakuncin Blackburn a League Cup a Stamford Bridge.