Chelsea ta karɓo Casadei da Moreira da ta bayar aro

Chelsea

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Chelsea ta karɓo Cesare Casadei daga Leicester City da Diego Moreira daga Lyon, waɗanda ta bayar aro.

Cesare, mai shekara 21, wanda ya sanya hannu kan yarjejeniya a Chelsea a Agustan 2022, ya buga wa Leicester City wasa 25 da cin kwallo uku a kakar nan.

Shi kuwa Moreira mai buga wa tawagar Portugal ta ƴan shekara 21, ya yi wa Lyon wasa tara, wadda take mataki na 16 cikin ƙungiyoyi 18 a gasar Ligue 1 ta Faransa.

Moreira ya koma Stamford Bridge kan fara kakar bana daga Benfica, ya fara wasa a Carabao Cup da Chelsea ta yi nasara a Wimbledon a cikin Agusta.

Chelsea tana mataki na tara da maki 31 a gasar Premier League, bayan da ta buga wasa 21.

Ranar Talata 23 ga watan Janairu, Chelsea za ta karɓi bakuncin Middlesbrough a karawar League Cup.

Daga nan ta karɓi bakuncin Aston Villa a wasan mako na 22 a gasar Premier League ranar Juma'a 26 ga watan Janairun 2024.