Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Kocin Focugal Santos ya ajiye aiki
Mai horar da Focugal Fernando Santos ya ajiye aikinsa, yan kwanaki bayan da Maroko ta fitar da kasarsa a gasar cin kofin duniya da ake yi a Qatar.
Mai shekaru 68 din ya yi rashin nasara 1-0 hannun Atlas Lions a zagayen Quarter-finals.
Santos ya shafe shekara takwas yana jan ragamar Focugal, inda ya ci musu kofin nahiyar Turai a 2016, da kuma na Uefa Nations League a 2019.
Sai dai an yi ta cece-kuce da ya ajiye kyaftin din kasar Cristiano Ronaldo, a wasannin karshe da kasar ta buga a gasar Qatar 2022.
Kocin ya ki fara wasa da Ronaldo ne a dalilin kalaman da ya yi bayan sauya shi a wasansu da Koriya ta Kudu.
Hukumar kwallon kafar Focugal a sanarwar da ta fitar, ta gode wa Santos kan namijin kokarin da ya yi tsawon shekaru takwas.
A yanzu hukuma ta FPF za ta shiga kasuwa don nemo wanda zai maye gurbinsa.