Chelsea ta dauko Chukuemeka daga Villa

An wallafa

Chelsea ta sanar da daukar dan wasan tsakiyar Aston Villa Carney Chukwuemeka kan fam miliyan 20.

Chukwuemeka wanda ke cikin tawagar yan kasa da shekara 19 ta Ingila da ta zamo gwarzuwa a gasar Turai a watan Yuli, ya rattaba hannu kan yarjejeniyar shekaru shida.

Dama baya cikin tawagar Aston Villa da ta ziyarci Australia, bayan da yaki saka hannu kan sabuwar yarjejeniyar da aka taya masa.

''Na ji dadi kuma na kagu in ganni cikin fili, in hadu da duka yan wasan in kuma yi kokari ganin na ci wasanni tare da lashe kofuna da Chelsea.'' In ji Chukuemeka.

Kafin Chelsea kungiyoyin Barcelona, da AC Milan da kuma Borussia Dortmund sun yi kokarin daukar dan wasan da koci Steven Gerrard yaso ya cigaba da aiki da shi a Villa Park.

Kazalika kafin shi Chelsea ta dauko Raheem Sterling daga Manchester City, da mai tsaron bayan Napoli Kalidou Koulibaly, sai kuma Cucurella daga Brighton farkon makon nan.