Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Iyalai da dama na cikin tsaka mai wuya sakamakon ambaliyar ruwa a birnin Damaturu
Daruruwan iyalai sun shiga cikin halin kaka-ni-ka yi a Damaturu, babban birnin jihar Yobe sakamakon aukuwar ambaliyar ruwa a ranar Laraba.
Yanzu haka suna rarrabe ne a gidajen 'yan uwa da abokan arziki, da makarantu da gidajen mai, bayan ambaliyar ruwa ta raba su da muhallansu .
Sai dai ana sa ran za a kai masu dauki a ranar Asabar, bayan da gwamnatin jihar ta tantance ire-iren tallafin da suke bukata.
Ambaliyar ruwan, wadda ta shafi wasu unguwanni a garin na Damaturu, babban birnin jihar Yoben, ta jefa jama'a da dama cikin tsaka mai wuya.
Ahmad Gaajimi, wanda wannan ambaliyar ta rutsa da gidansa, ya yi karin bayani:
“ Ba ka iya shiga da mota ko kus-kus don ka dauki kaya , duk kayan su na cikin ruwa, dakuna sun rushe”, in ji shi.
Malam Gaajimi ya ce ambaliyar ruwan ta shafi mutane fiye da 100 da ke ungwarsu kuma a cewarsa haka al'amarin yake a wasu unguwani biyu da ke birnin Damaturu.
Mamakon ruwan saman da aka yi tun ranar Talata zuwa Laraba ne ya haifar da ambaliyar ruwan kuma mazauna birnin sun ce har yanzu ba bu wani dauki da suka samu daga wurin mahukunta.
Tuni dai gwamnatin jihar Yobe ta yi shirin ko- ta- kwana don kaucewa lamura irin wadannan musaman tun bayan sanarwar da mahukantan jamhuriyar Kamaru su ka yi a kan cewa za su saki ruwan Lado dam.
Sai dai shugaban hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Yobe Mohamed Goje ya shaidawa BBC cewa sun fara daukar matakin kai dauki cikin gaggawa.
“ Mataki na farko shi ne a kai dauki cikin gaggawa domin lafiyar mutane, na biyu za mu je mu ga halin da mutane ke ciki, na uku akwai ungwar da hanyar ruwansu ba ta janye ba kuma inda za a bude domin ruwan ya fita zai shiga cikin wata ungwa ne, shiya sa mu ka sa shugaban karamar hukuma da hukumar muhali da su gyara hanyoyi da magudan ruwa.
A baya hukumar hasashen yanayi ya Najeriya ta yi hasashen cewa za a yi ambaliyar ruwa a wasu jihohin kasar sakamakon ruwan sama kamar da bakin kwarya da za a tafka abin da kuma ta ce zai haifar da ambaliyar ruwa.