Real Madrid na daf da lashe La Liga na 36 jimilla

An wallafa

Real Madrid ta kusan lashe La Liga na bana na 36 jimilla, bayan da ta ci Barcelona 3-2 ranar Lahadi a wasan hamayya na El Clasico a Santiago Bernabeu.

Jude Bellingham ne ya ci kwallo na uku daf da za a tashi a karawar da ya bai wa Real Madrid makin da take bukata.

Dan kwallon tawagar Ingila ya zura 17 a raga a bana, shi ne kan gaba a yawan cin kwallaye a La Liga tsakanin 'yan wasan Real Madrid.

Wannan shi ne karon farko da Bellingham ya ci kwallo a La Liga tun bayan 10 ga watan Fabrairu a wasa da Girona.

Hakan ya sa Real Madrid ta ci gaba da jan ragamar teburin La Liga da maki 81 da tazarar 11 tsakaninta da Barcelona mai rike da kofin bara.

Girona ce ta uku da maki 68 da kuma Atletico Madrid ta hudu da maki 61, bayan buga wasannin mako na 32.

Wasa daya aka ci Real Madrid a bana a La Liga, shi ne 3-1 da Atletico Madrid ta ci ranar 24 ga watan Satumbar 2024.

Real din ta ci wasa 25 daga karawa 32 a La Liga a kakar nan da canjaras shida da rashin nasara daya da cin kwallo 70 aka zura mata 22 a raga da maki 81.

Real Madrid wadda ta dauki Spanish Super Cup a bana, bayan cin Barcelona tana matakin daf da karshe a Champions League na bana mai 14 jimilla.

Ranar 30 ga watan Afirilu, Real za ta je Bayern Munich wasan farko daf da karshe a Champions League, yayin da za su buga karawa ta biyu a Spain ranar 8 ga watan Mayu.

Real Madrid tana da Champions League 14, yayin da Bayern Munich take da shida a tarihi.

Real Madrid ce kan gaba a yawan lashe La Liga mai 35, sai Barcelona mai 27 da Atletico Madrid ta uku mai 11.

Jerin kungiyoyin da suka lashe La Liga:

  • Real Madrid 35
  • FC Barcelona 27
  • Atletico Madrid 11
  • Athletic Bilbao 8
  • Valencia 6
  • Real Sociedad 2
  • Deportivo La Coruna 1
  • Sevilla FC 1
  • Real Betis 1

Wadanda ke kan gaba a cin kwallaye a La Liga

  • Artem Dovbyk Girona 18
  • Jude Bellingham Real Madrid 17
  • Ante Budimir Osasuna 16
  • Alexander Sorloth Villarreal 15
  • Borja Mayoral Getafe 15
  • Alvaro Morata Atletico Madrid 14
  • Vinicius Junior Real Madrid 13
  • Antoine Griezmann Atletico Madrid 13
  • Robert Lewandowski Barcelona 13
  • Gorka Guruzeta Athletic Bilbao 12
  • Hugo Duro Valencia 12

Wasannin La Liga da suka rage a gaban Real Madrid

Spanish La Liga Juma'a 26 ga watan Afirilu

  • Sociedad da Real Madrid

Spanish La Liga Asbar 4 ga watan Mayu

  • Real Madrid da Cadiz

Spanish La Liga Lahadi 12 ga watan Mayu

  • Granada da Real Madrid

Spanish La Liga Laraba 15 ga watan Mayu

  • Real Madrid da Alaves

Spanish La LigaSu 19 ga watan Mayu

  • Villarreal da Real Madrid

Spanish La Liga Su 26 ga watan Mayu

  • Real Madrid da Real Betis