An ci Man City da Aston Villa a wasan sada zumunta a Amurka

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Manchester City ta yi rashin nasara a hannun AC Milan da ci 3-2 a wasan sada zumunta, domin tunkarar kakar bada da suka buga a birnin New York.

Ɗan wasan da ya lashe takalmin zinare a bara a Premier League, Erling Haaland shi ne ya fara zura ƙwallo a raga, bayan da ya samu tamaula ta wajen Oscar Bobb.

AC Milan ta farke ta hannun Lorenzo Colombo, wanda ya kara na biyu ƴan dakika tsakani, haka suka je hutu Milan tana da 2-1.

Sai dai City ta farke ta hannun James McAtee, inda wasan ya koma 2-2, daga baya Marco Nasti ya ci wa Milan ƙwallo na uku.

City za ta je Florida, domin fafatawa da Barcelona a Camping World Stadium a birnin Orlando ranar 30 ga watan Yuli.

Ƙungiyar Ettihad za ta buga wasan sada zumunta na karshe a Columbus, Ohio, inda za ta kece raini da Chelsea ranar Asabar 3 ga watan Agusta.

A kakar da ta wuce City ta lashe Premier League, kuma na hudu a jere, wadda za ta buga Community Shield da FA Cup da League Cup da kuma Champions League a bana.

Aston Villa ta yi rashin nasara a hannun Columbus Crew

Aston Villa ta yi rashin nasara a wasan sada zumunta domin fuskantar kakar bana a hannun Columbus Cew da ci 4-1 a Amurka.

Ta buga wasan a karon farkon da Emi Buendia ya koma taka mata leda, wanda ya ji rauni tun daga watan Agustan 2023.

Ya shiga wasan tare da Amadou Onana da Ian Maatsen, waɗanda ta ɗauka a bana cikin minti na 63 a lokacin an gama cin Villa.

Ɗan wasa Hernandez ya ci wa Columbus ƙwallo biyu daga baya Villa ta zare ɗaya ta hannun Cameron Archer.

Daga nan Hernandez ya zura na uku rigis a karawar, sannan Dylan Chambost ya ci wa ƙungiyar da ke buga babbar gasar tamaula ta Amurka na huɗu a wasan.

Aston Villa za ta buga wasan gaba ranar Alhamis 1 ga watan Agusta da RB Leipzig a Red Bull Arena.

Sai ranar Asabar 3 ga watan Agusta Villa za ta karkare da karawa da Club America a Soldier Field.