Gane Mini Hanya: Batun ambaliyar ruwa a Jihar Jigawa

An wallafa

Hukumar bayar da agajin gaggawa ta Jigawa, SEMA ta bayyana damuwarta dangane da yadda ake samun ƙarin ƙananan hukumomi a jihar da ke ci gaba da fuskantar ambaliyar ruwa. 

Hukumar ta SEMA a Jigawan ta ce kawo yanzu kusan dukkan garuruwan da ke ƙananan hukumomi kusan huɗu ne ambaliyar ruwan ta shafa tare da shafe dukkan wata babbar hanya da ke yankunan. 

An dai fara samun ambaliyar ruwan ne a ƙarshen makon da ya gabata sakamakon ruwan da aka sako daga madatsar ruwa ta Tiga da ke karamar hukumar Bebeji a Kano. 

A filin Gane Mini Hanya na wannan makon, Khalifa Shehu Dokaji ya haɗa mana rahoto na musamman kan wannan batu.