'Jami'armu na cin gajiyar kashe-kashen da ake yi a Gaza'

    • Marubuci, Ahmen Khawaja
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC World Service
  • An wallafa

A lokacin da ɗaliba Achinthya Sivalingam mai karatun diogiri na biyu a jami'ar Princeton ta dauki matakin shiga zanga-zangar da aka gudanar aharabar jami'ar ranar 25 ga watan Afrilu, ba ta san cewa za a kamata ba, kuma hana ta zuwa makarantar tare da tsareta na rana guda ba.

“Mu fiye da 30 ne muka taru da misalin ƙarfe 07:00 na safe a harabar jami'ar domin gudanar da zanga-zangar lumana kan kisan kiyashin da ake yi a a Gaza,” kamar yadda ta shaida wa BBC.

Ɗalibar, mai shekara 28 na magana ne daga ɗakin kwananta na makarantar da ke jam'iar wadda ke jihar New Jersey, inda makomarta ke cikin halin rashin tabbas.

“Jami'armu ta zuba jari na maƙudan kudi a cibiyoyin Isra'ila,. Suna zuba jari wajen kashe-kashen da aka yi wa al;'ummar Gaza da Falasɗinawa,'' in ji Ms Sivalingam.

“Mun fito ne domin mu faɗa cewa abin da ake yi bai dace ba.’’

Tun bayan fara yaƙin Gaza a watan Oktoban bara, ɗalibai a Amurka suka riƙa gudanar da zanga-zanga, ta ƙin fita da yajin cin abinci, da kuma kafa tantuna don zanga-zangar baya-bayan nan.

Ɗaliban na buƙatar jami'o'insu su ƙaurace wa ikamfanoni da ɗaiɗaikun mutanen da ke ƙawance da ISra'ila.

Da farko sun fara kafa tanti ne a jami'ar Columbia da ke birnin New York ranar 17 ga watan Afrilu.

Bayan 'yan sanda sun tarwatsa tantunan, tare da kama ɗalibai fiye da 100, zanga-zangar ta watsu zuwa faɗin ƙasar.

Cikin mako biyu da suka gabata, fiye da ɗalibai 1,000 ne aka kama a sassan jami'o'in faɗin Amurka.

Ranar kame

“Wani daga cikinmu mun hallara a wani wuri a jami'ar domin nuna goyon bayanmu kan zanga-zangar da wasu ɗalibai ke yi a faɗin ƙasar ,” in ji Ms Sivalingam.

“A yayin da muka fara kafa tantuna, sai 'yan sanda suka zo.”

Ya kamata a ce gargaɗi suka yi mana, in ji ta, amma ta ce ba ta ji hakan daga gare su ba.

''Dukanmu muna da waƙe, kuma akwai hargisti sosai a wurin. Na ji lokacin da wani ɗan sanda ya ce ''Mu kama waɗancan biyun''.

An kama Ms Sivalingam tare da wani ɗalibin, mai suna Hassan Sayed, inda aka ɗaure hannayenta da kyau.

“Ina tunanin cewa hakan shi ne abin firgicin da na taɓa shiga, Na ji raɗaɗi a hannuna, har yanzu akwai alamar raunin ɗaurin a hannuna, na yi ta kuka sakamakon raɗaɗin da na ji,'' in ji ta.

Duka Ms Sivalingam da Mista Sayed an tsare su ne a wani ofishin 'yan sanda da ke wajen jami'ar inda aka tuhume su da ''abin da ba su da hurumin yi''.

“Wannan na faruwa da mu a jami'o'inmu da ɗakunan kwanan da muke zaune a ciki,” in ji ta.

An kuma hana su shiga jami'o'in, ciki har da ɗakunan kwanan ɗaliban, lamarin da ya sa ɗaliban suka rasa inda za su je.

'Yan sanda sun kai Ms Sivalingam zuwa dakin kwananta, inda suka jira a ƙofar, suka kuma gaya mata cewa ta tattara komatsanta cikin mintuna biyar domin su fitar da ita daga cikin makarantar.

“Na ɗauki duk abin da nake son ɗauka, ban ma samu damar ɗaukar abin da nake buƙata ba, saboda hankalina baya jikina,'' in ji ɗalibar.

Ta ce daga baya an ba su damar komawa ɗakunan ɗaliban bayan wasu sa'o'i, amma ta ce har yanzu an hana shu shiga cikin jami'ar, inda a yanzu suke fuskantar shari'ar ko ladabtarwa.

“Abin bai yi daɗi ba,sun kama mutum biyu kawai daga cikinmu waɗanda ba farar fata ba, daga cikin mutane bila adadin da suka yi zanga-zangar.”

Gabanin fara zanag-zangar, Jami'ar Princeton ta fitar da wata gajeriyar sanarwa ga ɗalibanta, inda take bayyana matsayinta kan 'yan faɗin albarkacin baki, da matakin da take ɗauka wajen magance zanga-zanga.

Jami'ar ta ce a yayin da take martaba '''yancin faɗar albarkacin baki ta kuma buɗe bincike kan duka lamurran'', tare da tabbatar al'ummar jami'ar cewa za a saurarin bahasin kowa kan korafin da yake son shigarwa.

A lokaci guda kuma jami'ar ta ce hakan bai kuma bayar da damar gudanar da zanga-zangar da ta zama barazana da muzgunaw ba.

Hassan Sayed, Ba'amurke ɗan asalin Pakistan da ke karatun digiri na uku a fannin tsimi da tanadi, da kuma ke koyarwa a jami'ar Princeton, an kama shi ne tare da Ms Sivalingam.

“A cikin minti da fara zanga-zangar, aka ɗaura mana ankwa, aka kuma ce masa an hana su zuwa jami'ar'', kamar yadda ya shaida wa BBC.

Mista Sayed ya ce har yanzu yana ƙoƙarin gano abin da ya faru kuma yana jin ''damuwa da dama'', tun bayan kama shi.

“Amma abin da ya fi haka muni, shi ne ina son mayar da hankali kan yadda a halin yanzu babu jami'ar da ke aiki a Gaza. Na yi zanga-zanga ne domin nuna goyon bayana gare su, a yayin da suke fama da rugujewar abubuwan rayuwa da na ilimi,” in ji shi.

Hankula sun fara tashi a jami'o'in Amurka tun harin ranar 7 ga watan Oktoba da Hamas ta kai Isra'ila, lamarin da ya yi sanadin mutuwar kusan mutum 1,200.

Harin da ya fuskanci ramuwar gayya daga bangaren Isra'ila ta hanyar ƙaddamar da hare-hare a Gaza, waɗanda suka yi sanadin kisan fiye da Falasɗinawa 34,000.

“Abu ne mai sosa rai, idan ka kalli bidiyoyin yadda mutane ke shan wahala a Gaza tun bayan harin na Oktoba,” in ji Mista Sayed.

“A ɗaya ɓangaren kuma ga wasu mutane da ke zuba jari da ke taimaka wa kisan kiyashin daake yi a Gaza, ciki watakila har da jami'ar Princeton.”

Masu sukar Isra'ila sun aha faɗin cewa ayyukan sojinta a Gaza sun haifar da kisan kiyashi a yankin, kuma Afirka ta Kudu ta kai batun Gaban Duniya.

Isra'ila ta dage cewa sojojinta na aiki ne ''cikin tsafta'' tare da zargin Hamas da niyar kisan kiyashin.

Su bayyana, su daina tare da janye jikinsu

“Muna buƙatar abubuwa uku daga jami'o'inmu: Su bayyana, karkatar tare da janye kansu,” in ji Ms Sivalingam.

Ta ce abin da ɗaliban ke so shi ne jami'ar Princeton ta bayyana irin jarin da take zuba wa a Isra'ila, kuma dole da daina abin da take yi ta hanyar katse alaƙa da Isra'ila.

Daliban sun ce kamfanonin da ke hada-hadar kasuwanci da Isra'ila na ƙara dagula yaƙin da ake yi a Gaza - kuma jami'o'in na zuba jari a kamfanonin.

Jami'o'in na bayar da tallafin kuɗin bincike da na tallafin karatu daga ribar biliyoyin daloli da suke samu a jarin da suke zubawa a kamfanonin.

Sun mallaki hannayen jari masu yawa a manyan kamfanoni irin su Amazon da Microsoft, inda suka amfani da ribar da suke samu wajen gudanar da wasu ayyuka.

Misi Sivalingam tare da sauran ɗalibai na fargabar cewa jami'ar Princeton ka iya zuba jari a ƙera makamai wanda za ta iya samun riba daga yaƙin Gaza.

BBC ta tuntubi Jami'ar Princeton don jin bahasin zargin ɗaliban, inda jami'ar ta yi musu ishara da ƙa'idojin zuba jari na jami'ar da suka yi tanadin cewa babban muradin saka hannun jari na jami'ar shi ne "samar da riba mai dogon zango daga zuba jarin".

Jami'ar Princeton ta ce ƙa'idojinta sun bayyana ƙarara cewa "akwai dokoki masu ƙarfi dasuka haramta wa jami'ar shiga lamurran da suka jiɓanci siyasa ko abubuwan da suka shafi ƙasashen waje,'.

A wani taro da jami'ar ta gudanar cikin watan Fabrairu, shugaban jami'ar, Christopher Eisgruber ya ce jami'ar ba za ta ɗauki wani mataki a kan ƙorafin dalibai na kiran daina zuba jari a kamfanonin da ke da alaƙa da Isra'ila har sai an cimma cikakkiyar yarjejeniya a kan batun.

‘Ba lallai na kammala karatuna ba’

Zanga-zangar ba ta yi wa Ms Sivalingam da Mista Sayed, daɗi ba, bayan kama su da aka yi, a yanzu sunayensu sun shiga jerin mutanen da aka kama a hukumance.

“A yanzu fuskata ta yaɗu zuwa ko'ina. Abun ya zama tashin hankali,” in ji Ms Sivalingam.

A wannan wata ne ya kamata ta kammala karatu, to amma yanzu tana fuskantar shari'a.

Amma ta ce ba za ta bari hakan ya sage mata gwiwa ba.

“Na yi amfani da 'yancina wajen gudanar da zanga-zanga. Ina ganin wannan lokacin da ya kamata Amurka ta ɗauki matsayi game da wace ce ita, kuma me take son zama, a kan waɗanan manyan rigingimu.”