Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Abin da ya kamata ku sani kan wasan Liverpool da United
Liverpool ta karbi bakuncin Manchester United, domin buga wasan mako na 26 a gasar Premier League a Anfield ranar Lahadi.
Ranar 22 ga watan Agusta United ta ci Liverpool 2-1 a Old Trafford a wasan farko da suka fafata a bana.
Jadon Sancho da kuma Marcus Rashford ne suka ci wa United kwallayen daga baya Mohamed Salah ya zare daya saura minti tara a tashi daga wasan.
Liverpool tana ta shida a teburin Premier da maki 39, United kuwa tana ta uku mai maki 49.
A karawar ta ranar Lahadi a Anfield, Liverpool ba ta da wasu sabbi 'yan wasa da suka yi rauni kawo yanzu.
Amma har yanzu Arthur Melo da Thiago da Luis Diaz da kuma Joe Gomez na jinya.
United na auna koshin lafiyar mai tsaron baya, Luke Shaw, wanda bai buga wasan da kungiyar Old Trafford ta ci West Ham a FA Cup.
Jadon Sancho bai da lafiya, yayin da Donny van de Beek da Christian Eriksen da kuma Anthony Martial ke jinya.
Karawa tsakanin kungiyoyin biyu:
Liverpool ba ta yi rashin nasara ba a wasa shida da United a gida ba, wadda ta ci uku da canjaras uku - yun bayan 1-0 da United ta ci a Janairun 2016.
Sau takwas United ta yi wa Liverpool gida da waje a Premier League, watakila ta kara yin haka a bana a karon farko tun bayan 2015-16.
Kwallo daya United ta zura a raga a zuwa bakwai baya da ta yi Anfield - ta kasa zura koda daya a wasa hudu a jere a dukkan fafatawa a bayan nan.
Wasa hudu United ta yi nasara daga 17 da ta fuskanci Jurgen Klopp a Liverpool a dukkan haduwa da canjaras bakwai da shan kashi shida.
Liverpool
Liverpool ta ci wasa uku daga hudun da ta buga a bayan nan, bayan da ta kasa cin koda daya ne daga hudun da ta yi a 2023.
Watakila a kasa doke Liverpool a karo na biyar a jere a lik a karon farko a kakar bana.
Ta hada maki 27 a gida da kuma 12 a waje - rarar kwallaye mai yawa fiye da sauran kungiyoyin Premier League.
Virgil van Dijk ya ci kwallo 20 Premier League, mai tsaron bayan da yake kan gaba waje zura kwallaye da yawa a raga tun da ya koma Anfield daga Southampton a 2015.
Saura kwallo daya Salah zai ci ya yi kan-kan-kan da yawan wadanda Robbie Fowler ya ci wa Liverpool a Premier League mai 128 a raga.
Salah kan ci kwallo akalla 20 a dukkan gasa a kowacce kaka shida a Liverpool
Dan kwallon Masar ya ci United kwallo takwas - Alan Shearer ne kan gaba a dan wasan da ke kan gaba a cin United kwallo 10.
Diogo Jota ya kasa cin kwallo a wasa 26 a dukkan fafatawa - rabon da ya ci kwallo tun 2-2 da Manchester City a Premier League ranar 10 ga watan Afirilu.
Manchester United
Manchester United ta yi rashin nasara wasa daya daga 11 da ta yi a Premier League, shine 3-2 a gidan Arsenal, wadda ta ci takwas da canjaras biyu.
United ta hada maki 23 tun bayan kammala gasar kofin duniya a Qatar - wadda ta kaita samun maki daya bayan gasar kofin duniya.
Watakila ta hada maki 50 bayan karawa 25 a Premier League karo na biyu tun bayan Sir Alex da ya yi ritaya. Jose Mourinho ya hada 53 a 2017-18, inda ta yi ta biyu a gasar.
United ta ci wasa shida daga 12 da ta yi a waje daidai da irin kwazon da ta yi a bara kenan.
Kungiyar Old Trafford kan zura kwallo a raga a dukkan wasa 15 da ta yi a kron farko tun bayan 17 da ta yi haka tsakanin Fabrairu zuwa Oktoban 2020.
Marcus Rashford ya ci Liverpool kwallo shida tun daga kakar 2017-18, irin yawan na Harry Kane, amma dan wasan United bai taba cin Liverpool a Anfield ba.
Rashford ya ci kwallo 10 a wasa 10 a Premier League da zura kwallo a karawa biyar baya. 'Yan wasa uku ne suka ci a wasa shida a jere a United da suka hada da Ruud van Nistelrooy da Eric Cantona da kuma Cristiano Ronaldo.