Ku so Putin, Ku tsani Faransa: In ji magoya bayan Rasha a Afirka

Zanga-zanga a Mali

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Wasu masu goyon bayan sojojin haya na Rasha
An wallafa

An gano wata tawagar magoya bayan Rasha da masu rajin ƙin ƙasashen yamma, ƙasashe Afirka da ke magana da Faransanci.

Ana kiransu Russosphère, abin da ya jefa makomar turawan mulkin mallakar turawan Faransa cikin yanayin rashin tabbas, Suna yawan ziga Vladimir Putin kuma sun kiran sojin Ukraine ‘yan 'Nazi' da kuma 'Shaiɗanu'.

Kuma suna yawan zuga sojojin haya na Rasha, suna basu bayanai kan aikin da suke yi da waɗanda suke son aiki tare da su.

Masana sun ce irin waɗan nan bayanai sun janyo rashin yarda tsakanin kasashen Afrikan da na yamma, kuma ya janyo ƙarancin taimako da Ukraine ke samu daga nahiyar.

Wani aiki da aka yi cikin dabara, wani kamfanin fasaha wanda ya bibiyi tawagar, ya yi aiki da ɓangaren bankaɗo labaran ƙanzon kurege, sun kuma gane wai abin mamaki na adadin mutanen da ke tare da su, kuma ciki har da wani dan siyasar ƙasar Belgium mai shekara 65 wanda ya kira kansa mai ra’ayin tarayyar Soviet.

Kare Rasha da godiya ga mayaƙan Wagner

BBC
Bayanan hoto, Wallafe-wallafen 'yan Mali magoya bayan Rasha

'Russosphère' ta bayyana kanta a matsayin ƙungiya kare muradan Rasha.'

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Ta haɗa masu amfani da kafafen sada zumunta daban-daban, an ƙirƙireta ne a 2021, amma a watan Fabirairun 2022 aka ƙaddamar da ita, 'yan kwanaki gabanin ƙaddamar da mamayar Rasha a Ukraine. Cikin gaggawa ƙungiyar ta samu magoya baya 80,000.

Bayan mamayar, an sanya wa kafafen yaɗa labarai na Rasha takunkumi da kuma hana su kataɓus a kafafen sada zumunta.

Russosphère bata ciki kuma nan da nan ta koma kan Facebook da lamuranta, akan samunta a YouTube da Twitter bayan Telegram da VK – wani sabon gidan Rasha a Facebook.

Kyle Walter shi ne shugaban wata hukumar binciken sirri ta Amurka. Sun yi amfani da wata fasahar zamaninsu wajen bibiyar wanda ya ke gudanar da ayyukan ƙungiyar, wani mutum da ake kira Luc Michel.

A baya, Michel ya yi aiki domin tabbatar da an kaɗa ƙuri’un da suka dace ga Rasha, a yankin da Rasha ta mamaye na Ukraine, kuma yana da alaƙa da ƙungiyar "Merci Wagner" da ke goyon bayan ayyukan sojin haya na Rasha.

Mun tuntuɓi Michel kuma ya amince ya tattauna kan Russosphère. Ya ce mana shi ne ya ƙiirkireta, amma ya yi iƙirarin ba ta samun wani taimakon kuɗi daga Rasha, yana ce wasu mutane ne na daban ke ba ta kuɗi.

Ya dage kan cewa ba shi da wata alaƙa da Wagner da kuma shugabanta Yevgeny Prigozhin.

"Ni ina gudanar da aiki na ne na yaƙi a intanet.... yaƙin kafafen sadarwa...shi kuma Prigozhin na gudanar da ayyukan soji," in ji shi.

Luc Michel

Asalin hoton, Luc Michel

Bayanan hoto, Luc Michel an ɗan san shi a Turai, amma ya bayyana kan shi a nahiyar Afrika

Abin koyin Muammar Gaddafi da Vladimir Putin

Labarin Michel ba wani abin da aka saba ba ne ga Abokansa na Afrika.

Na haife shi a 1958, a fara siyasa ne tun yana ɗan ƙarami, yana da ra'ayin ba irin na dimokradiyya ba a gida Belgium, daga baya a matsayinsa na mabiyin Jean Thiriart tsohon wanda ya yi aiki da Nazi wanda suka haɗa kai domin yaƙar Amurka.

Aikinsa ya kai shi Libya ya yi aiki tare da Muammar Gaddafi, daga baya kuma ya koma Burundi a matsayin mashawarci ga shugaba Pierre Nkurunziza.

BBC
Bayanan hoto, Tattaunawar Michel da shugaban CAR

Daga kafafen yaɗa labarai zuwa kan tituna

Yana da wuya ka iya gano tasirin wani ƙoƙari rashin gano gaskiya, amma a Afrika saƙon masu goyon bayan Rasha ina jin shi sosai – ana jin muryarsu yadda ya kamata kamar inda masu sharhi suka yi bayani.

"Nasarar da mutane irinsu Luc Michel suka samu na da alaƙala adawar da yake yi da Faransa. Kamar yadda Kevin Limonier wani Farfesa a Jami'ar Paris ya bayyana.

"Kafafen yaɗa labaran Rasha na daga cikin abubuwan da suka taimaka aka tisa ƙeyar dakarun Faransa daga ƙasashen Sahel, musamman Burkina Faso," in ji Ulf Laessing, na gidauniyar the Konrad Adenauer.

A 2013, an kai wasu dakarun Faransa 5,000 Mali da Burkina Faso da Chadi da Nijar da kuma Mauritaniya domin yaƙi da masu iƙirarin jihadi.

Amma a bara, sun fice daga Mali kuma suna ci gaba da shirin ficewa daga Burkina Faso.

AFP

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Tutar Rasha a wata zanga-zanga da aka yi a watan Oktoban 2022

Beverly Ochieng daga sashen bibiya na BBC ya amince: "an ta ɗaga tutar Rasha a yayin zanga-zangar Mali da Burkina Faso da Niger da kuma Chadi, wannan kuma duka na cikin shirin ɗaukaka Rasha.”

A Burkina Faso, masu zanga-zanga sun rika kai hari kam ofishin jakadancin Faransa inda aka rika jin neman alaƙa tsakanin Ouagadougou da Moscow.

Abin da suke neman yi su Luc Michel shi ne "ina ganin suna neman maye gurbin Faransa da Rasha a duka nahiyar Afrika,” ya shaida wa BBC.

"Hasashen tasirin yadda labarai ke aiki sun wuce tunanin mutum," in ji Kevin Limoner. Amma abin da ya bayyana a zahiri: irin waɗan nan ayyuka na damun kasashen Yamma.