Ƙalubalan da Tinubu zai fuskanta a mulkinsa

Bayanan bidiyo, Taba hoton sama ku kalli bidiyo:
Ƙalubalan da Tinubu zai fuskanta a mulkinsa
An wallafa

Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya karɓi rantsuwar kama aiki a daidai lokacin da ƙasar ke fuskantar matsaloli daban-daban.

Yanzu bari mu dubi irin kalubalen da Bola Tinubu zai fuskanta a ɓangaren tsaro, wadda ya addabi kasar da ta fi kowacce yawan jam'a a Nahiyar Afirka.

Duka yankunan Najeriya na fuskantar akalla matsalar tsaro ɗaya.

Ana fuskantar matsalar ƴan bindiga a arewa maso yamma, ga matsalar ƴan ta’adda a yankin arewa maso gabas, da rikicin manoma da makiyaya a arewa ta tsakiya, ga kuma ƴan aware da ke yankin kudu maso gabashin ƙasar.

Haka nan, akwai ƴan kungiyoyin asiri a kudu masu yamma, da kuma masu tayar da kayar baya da fashin jirgin ruwa da satar mai a kudu maso kudu.

Akwai kuma matsalar satar mutane don neman kudin fansa, wadda ta zama ruwan-dare a sassa daban-daban na kasar.

Ta yaya sabon shugaban kasar zai shawo kan wadannan matsalolin na tsaro?

"Akwai bukatar a dubi tsaro ta wani bangare," a cewar masanin tsaro Kabir Adamu. "Ta yaya za mu iya shigo da al’umma cikin harkar tsaron kasa?

"Ana sa ran Tinubu zai bai wa jihohi ƙarin damar saka hannu sosai a cikin harkar tsaron kasa.

"Batu na karshe shi ne buƙatar da ke akwai na samun wani tsari na musamammn domin inganta yanayin tarbiya da sauya tunanin ƙasar."

"Mafi yawan matsalolin tsaro da muke fuskanta yanzu sun samu ne sakamakon durkushewar tsarin tarbiyarmu."

Tattalin arziki

Najeriya na fuskantar barazanar tattalin arzikin da ba ta taɓa ganin irinta ba, inda ake ci gaba da samun hauhawar farashin kaya.

Kasar na fama da rashin ci gaban tattalin arziki, ga karyewar darajar kuɗin naira, da kuma matsalar tsadar rayuwa.

Bugu da ƙari, akwai yawan adadin marasa aikin yi, wanda ya sa kusan rabin mutanen da ke ƙasar ke cikin ƙangin talauci.

Wace hanya sabon shugaban kasar zai bi wajen magance waɗannan matsalolin?

Masanin tattalin arziki Wilson Erumebor na ganin: "Daya daga cikin matakan da nake ganin suka kamata a ɗauka cikin gaggawa shi ne saka ƙwararru a cikin gwamnati.

"Ya kamata ƙudurorin gwamnati su taɓa rayuwar talakawan kasar. Daya daga cikin abubuwan da za a yi shi ne a magance matsalar satar man fetur, a kuma tabbatar da cewa gwamnati ta bunƙasa yawan kudin shiga."

Ilimi

A cewar Hukumar Ilimi da Al’adu ta Majalisar Dinkin Duniya UNESCO, kimanin yara miliyan 20 a Najeriya ba sa zuwa makaranta. Adadin na daga cikin mafi yawa a duniya.

Karatun jami’a ya fuskanci barazana saboda yajin aikin malamai karkashin kungiyar ASSU. Kungiyar ta yi yajin aiki sau biyar karkashin mulkin Muhammadu Buhari.

ASUU ta yi yajin aiki na kusan adadin shekara biyar daga lokacin da aka kafa dimokuradiyya a shekarar 1999.

Ta wace hanya sabon shugaban kasa zai iya kiyaye afkuwar wani yajin aikin?

"Ya kamata duk mu yi kira ga gwamnati mai shigowa da ta dauki karatun jami’a da matukar muhimmanci," in ji Farfesa Emmanuel Victor Osodeke, shugaban ƙungiyar ASUU.

"Duk ƙasar da ta yi wasa da harkar ilimi za ta gayyaci rashin tsaro. Kuma halin da muke ciki ke nan yanzu. Idan suka samu ingantaccen ilimi tare da ayyukan yi, ba za su aikata wadannan abubuwa ba."

Lafiya

Rashin samar da isassun kudi a fannin kiwon lafiya, da rashin ingantattun kayan aiki, da kuma rashin albashi mai kyau sun haddasa hijirar ma’aikatan lafiya da dama zuwa wasu kasashen duniya.

A cewar ƙungiyar likitoci masu neman kwarewa a watan Nuwamban bara, likitocin da ke wannan matakin da suka rage a kasar ba su wuce 10,000 ba.

Masani kan harkokin lafiya Dr. Salmon Oladapo ya ce: "Ya kamata a inganta halin rayuwar ma’aikatan lafiya tare da kara masu albashi.

"Kuma ya kamata gwamnati ta kara kudin da take ware wa bangaren lafiya, ya kai kashi 15 na kasafin kudin kasa."

Mafi yawan wadannan matsalolin abubuwa ne da gwamnatocin baya suka fuskanta, amma ‘yan Najeriya na sa ran sabon shugaban kasarsu zai yi aiki tuƙuru don magance su cikin gaggawa.

Bola Tinubu

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Bola Tinubu