Wane ne Kashim Shettima?

Asalin hoton, Kashim Shettima Facebook
A ranar Lahadi 10 ga watan Yuli ne ɗan takarar shugaban Najeriya ƙarƙashin Jam'iyyar APC Bola Ahmed Tinubu, ya zaɓi tsohon gwamnan Jihar Borno Kashim Shettima a matsayin mataimakinsa a takarar shugaban ƙasa.
Shettima ya bayar da muhimmiyar gudunmawa a yaƙin neman zaɓen Tinubu har Jam'iyyar APC ta samu nasara.
Kashim Shettima gogaggen ma’aikacin banki ne kuma ɗan siyasa wanda a yanzu haka shi ne Sanata mai wakiltar yankin tsakiya na Jihar Borno.
Shettima ya yi gwamnan Jihar Bornon arewa maso gabashin Najeriya sau biyu, tun daga 2011 zuwa 2019.
Ya yi karatun digirinsa na farko da na biyu a Jami’ar Maiduguri da Jami’ar Ibadan.
Bayan ya kammala karatu ne ya fara kasuwanci da aikin banki, inda daga baya ya haye muƙamai da yawan a bankuna daban-daban.
A tsakiyar shekarun 2000 ne, Shettima ya zama manajan Bankin Zenith a Maiduguri kafin daga baya ya bar aikin ya samu muƙami a gwamnatin Gwamna Ali Modu Sheriff a 2007.

Asalin hoton, Twitter/Shettimma
Ya shafe shekara huɗu ana tafiya da shi a waccar gwamnatin, sai ya tsaya takarar gwamnan Borno a shekarar 2011, sannan ya yi tazarce a 2015.
Bayan ya kammala wa’adinsa biyu ne sai ya tsaya takarar ɗan majalisar dattijan Najeriya kuma ya yi nasara a 2019.
An haifi Kashim Shettima a Maiduguri, babban birnin Jihar Borno.
Ya fito ne daga zuri’ar gidan Alhaji Shettima Mustafa Kuttayibe.
End of Karin wasu labaran da za ku so ku karanta

Asalin hoton, Twitter/Kashim Shettima
Ga wasu abubuwan a game da shi a taƙaice
- An haife shi ranar 2 ga watan Satumban 1966.
- Ya yi makarantar firamare ta Lamisula a Maiduguri daga 1972 zuwa 1978.
- Ya fara karatunsa na sakandire a Government Community Secondary School, Biu, daga 1978 zuwa 1980.
- Daga bisani ya koma Makarantar Sakandiren Kimiyya ta Gwamnati a Potiskum inda ya kammala a 1983.
- Ya yi digiri a fannin Tattalin Arzikin Harkar Noma a Jami’ar Maiduguri a 1989.
- Ya yi digiri na biyu a a fannin Tattalin Arzikin Harkar Noma a Jami’ar Ibadan a 1991.
- Shettima ya yi aikin koyarwa a fannin Tattalin Arzikin Harkar Noma a Jami’ar Maiduguri, daga 1991 zuwa 1993.
- Ya yi aikin banki da bankuna da dama daga tsakanin 1993 zuwa 2007.
- Ya yi kwamishinan kudi da tattalin arziki na jihar Borno a 2007.
- Ya yi kwamishinan ƙananan hukumomi a 2008 da kwamishinan ilimi a 2009 da kwamishinan harkar noma da ma’adinai da kuma kwamishinan lafiya har zuwa 2011, inda daga nan ya tsaya takarar gwamna.
- Ya lashe zaben gwmanan jihar a 2011 sannan ya sake yin nasarara karo na biyu a 2015.
- A watan Fabrairun 2019 kuma ya lashe zaben dan majalisar dattijai mai wakiltar Bornon ta tsakiya.
- Yana da mace ɗaya Nana Shettima da ƴaƴa uku, mata biyu, namiji ɗaya.











