Super Eagles za ta kara da Zimbabwe ranar Lahadi

An wallafa

Tawagar ƙwallon ƙafa ta Najeriya Super Eagles ta sauka a Rwanda a sanyin safiyar Asabar, domin buga wasa da Zimbabwe a neman shiga gasar cin kofin duniya da za a yi a 2026.

Najeriya za ta buga wasa na biyu a cikin rukuni na uku bayan tashi 1-1 da Lesotho ranar Alhamis.

A tsakar daren Asabar Najeriya ta yi shatar jirgin sama daga filin jirgin sama na Victor Attah zuwa Kigali.

Daga nan ne za ta shiga motar da za ta yi awa biyu zuwa Butare, inda za ta fafata a filin wasa na Huye, mai cin 'yan kallo 20,000.

Zimbwe tana buga wasanninta a Rwanda saboda ba ta da filin da yake da darajar da ake bukata, wadda ta tashi ba ci a wasan farko da Rwanda.

Super Eagles za ta kece raini da Zimbabwe a filin wasa na Huye da misalin kafe 1:00 na rana agogon Najeriya - karfe 3:00 agogon Rwanda.

Souleiman Ahmed Djama daga Djibouti, shi ne rafali, wanda zai samu mataimaka da suka hada da Liban Abdoulrazack Ahmed, da Rachid Waiss Bouraleh, da Mohamed Diraneh Guedi a matakin masu jiran ko-ta-kwana.