Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Arsenal na iya doke ƙungiyoyin Premier a zawarcin Declan Rice
Dan wasan tsakiya na West Ham Declan Rice, shi ne na farko da Arsenal ke son saye a bazarar nan, kuma akwai alamun cewa Gunners ɗin za su iya doke Chelsea da Manchester City da Manchester United wajen sayen ɗan wasan na Ingila. (Evening Standard)
Haka ita ma Manchester United tana sa ido kan ɗan gaban Eintracht Frankfurt Randal Kolo Muani na Faransa tare da matashin ɗan gaban Atalanta Rasmus Hojlund daga Denmark ko da burin United na sayen Harry Kane, bai tabbata ba. (Manchester Evening News)
Ita kuwa Real Madrid ta karkata ne kan matashin ɗan wasan tsakiyar Borussia Dortmund Jude Bellingham, a matsayin wanda ta fi son ganin ta saya, bayan shi kuma kulob ɗin na son sayen ɗan bayan Chelsea Reece James daga Ingila. (AS)
Wataƙila United ta rasa damar sayen ɗan wasan tsakiya na ƙasar Austria, Marcel Sabitzer bayan aron sa saboda sabon kociyan Bayern Munich, Thomas Tuchel zai iya yanke shawarar riƙe shi. (Sun)
Bajamushe Julian Nagelsmann, mai shekara 35, da Mauricio Pochettino ɗan Argentina mai shekara 51, wani daga cikin su na iya maye gurbin Antonio Conte a matsayin sabon kocin Tottenham - sai dai kuma dukkansu sai sun jira ko za su samu aikin horar da Real Madrid a bazara. (90min)
Tsohon kociyan Sifaniya Luis Enrique, ya ce zai so ya zama manajan wata ƙungiya ta Premier, amma fa sai ƙungiyar da za ta iya taɓuka wani abin kirki. (Cadena SER )
Ɗan wasan tsakiya na Jamus Ilkay Gundogan, zai bar Manchester City domin tafiya Barcelona a kyauta cikin ƙarshen kakar nan, kasancewar kwanturaginsa da Cityn ya ƙare. (Football Insider)
Don haka ne yanzu Barcelona za ta ci gaba da tattaunawa da Gundogan bayan ta cimma yarjejeniyar baki a kan ɗaukar ɗan bayan Athletic Bilbao na Sifaniya Inigo Martinez. (ESPN)
Barcelona za ta yi yin gogayya da Arsenal da Chelsea a kan matashin ɗan wasan gaba na ƙasar Brazil Vitor Roque da ke buga wa Athletico Paranaense mai shekara 18. (Sport)
Manchester City da Paris St-Germain sun fara taya matashin ɗan bayan ƙungiyar Hajduk Split Luka Vuskovic ɗan ƙasar Croatian mai shekara 16. (90min)
David de Gea, ya yi watsi da tayin sabon kwanturagin da Manchester United ta yi masa. (Athletic)
Haka shi ma, Marcus Rashford ya yi watsi da rahotannin cewa ya nemi sabon kwanturagin da Manchester United za ta rinƙa biyansa albashin fam dubu 500 a duk mako, a cewarsa, shirme ne kawai. (Independent)
United na shirin tattaunawa da Rashford a kan sabunta kwanturagin nasa kafin ƙarshen kakar nan. (ESPN)
Mahaifin Ansu Fati yana son ɗan nasa mai shekara 20 ya bar Barcelona cikin wannan kaka, saboda ba a sanya shi a wasanni sosai. (Athletic )