Messi ya ci wa Argentina kwallo sama da 100

An wallafa

Kyaftin Lionel Messi ya ci wa Argentina kwallo sama da 100, bayan da Argentina ta doke Curacao 7-0.

Mai shekara 35 shine ya fara zura kwallo a raga a minti na 20 da fara wasan, kuma na 100 da ya ci Argentina kenan a karawar da suka yi Santiago del Estero.

Messi ya kara cin biyu tun kafin hutu, kenan kwallo uku rigis ya zura a raga, karo na bakwai da ya yi wannan bajintar a Argentina.

Dan wasan Chelsea, Enzo Fernandez shima ya zura kwallo a wasan da Argentina ta gabatar da kofin duniya da ta lashe a gaban 'yan kallo sama da 42,000

Wannan shine wasa na biyu da Argentina ta buga tun bayan da ta lashe kofin duniya a Qatar a 2022, bayan doke Faransa a bugun fenariti.

A makon jiya Messi ya ci kwallo na 800 a sana'arsa ta murza leda - ya kuma zura na 99 a Argentina a karawar da ta ci Panama 2-0 a Buenos Aires a wasan sada zumunta.

Mai taka leda a Paris St-Germain ya ci wa Argentina na 100, bayan da ya samu kwallo daga dan wasan Villarreal, mai taka leda aro a Tottenham, Giovani lo Celso.

Minti uku tsakani Nicolas Gonzalez ya ci kwallo, sannan ya bai wa Messi ya zura a raga na uku a karawar.

Fernandez ne ya zura na hudu, sannan Lo Celso ya kara bai wa Messi shi kuma ya ci na biyar a minti na 37, sannan na uku rigis da ya ci.

Angel di Maria da Gonzalo Montiel ne suka zura sauran biyu a raga, an kuma taya Messi ci gaba da kafa tarihin yawan cin kwallaye a tawagar Argentina.

Gabriel Batistuta shine na biyu mai kwallo 56 a Argentina, Messi yana da 102 kenan.

Kyfatin din Argentina shine na uku a yawan ci wa tawaga kwallaye a duniya, bayan dan wasan Portugal, Cristiano Ronaldo mai 122 da na Iran Ali Daei mai 109.