Cunha ya ci Chelsea kwallo uku rigis a Stamford Bridge

An wallafa

Matheus Cunha ya ci Chelsea kwallo uku a gasar Premier League ranar Lahadi, bayan da Wolverhampton ta yi nasara da cin 4-2 a Stamford Bridge.

Chelsea ta buga wasan mako na 23 a babbar gasar tamaula ta Ingila, wadda ta sha kashi, sannan Wolves ta maye gurbinta.

Cole Palmer ne ya fara ci wa Chelsea kwallo a minti na 19 da fara wasa, sai dai minti uku tsakani Matheus Cunha ya farke.

Daf da za a yi hutu ne Wolverhamton ta kara na biyu a raga, bayan da Chelsea ta ci gida ta hannun Axel Disasi.

Bayan da suka yi hutu ne suka koma wasa Cunha ya kara na uku na biyu da ya zura a raga, sannan ya ci na hudu na uku da ya zura a raga rigis a Stamford Bridge.

Saura minti hudu a tashi daga fafatawar Chelsea ta zare daya ta hannun Thiago Silva.

Da wannan sakamakon kungiyar da Gary O'Neil ke jan ragama ta koma ta 10 matakin Chelsea, wadda ta yi kasa matsayi na 11 da tazarar maki daya, bayan wasa 23.

Ranar 7 ga watan Fabrairu Chelsea za ta je Aston Villa, domin buga zagaye na biyar a FA Cup.

Daga nan ne kungiyar Stamford za ta je Selhurst Park, domin fafatawa da Crystal Palace a wasan mako na 24 ranar Litinin 12 ga watan Fabrairu.