Ku San Malamanku tare da Malama Ruqayya matar Sheikh Daurawa

Bayanan bidiyo,
Ku San Malamanku tare da Malama Ruqayya matar Sheikh Daurawa
An wallafa

An haifi Malama Ruqayya Abbas Usman a unguwar Kofar Mazugal a cikin birnin Kano a 1971.

Ta shaida wa BBC cewa ta fara karatu a hannun mahaifanta, musamman mahaifiyarta, wadda ta fara karatun allo a wajenta. Sannan ta halarci makarantar allo ta Mallam Musa a unguwar Kofar Mazugal da makarantar Arzai ta Sheikh Na'ande. Ta kuma yi makarantar Islamiyya ta Nahdatul Islam.

Sannan ta yi karatu a hannun maigidanta, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa a fannin Kur'ani da Tafsir da Tauhidi da Fikhu da Sira da sauransu.

A 1985, Malama Ruqayya Abbas ta kammala sakandire ta Women Arabic Teachers College, daga sai ta shiga Kwalejin Nazarin Shari'a ta Aminu Kano, inda ta karanta fannin nazarin harsunan Larabci da Hausa.

Ta kuma yi karatun digirinta ta farko a wata Jami'ar Sudan mai mazauni a Najeriya. Ta kuma yi digiri ta biyu a Alwefaq International University reshenta da ke Najeriya.