Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
West Ham ta kammala sayen Fullkrug daga Dortmund
West Ham ta kammala sayen ɗan wasan tawagar Jamus, Niclas Fullkrug daga Borussia Dortmund kan fan miliyan 27, kan kwantiragin kaka hudu.
Ɗan wasan mai shekaru 31, wanda ya koma Dortmund daga Werder Bremen a bara, ya ci kwallo 15 a wasa 46 a 2023-24, wadda ta yi ta biyu a Champions League.
Haka kuma ya ci wa tawagar Jamus ƙwallo biyu, wadda ta karɓi bakuncin Euro 2024, wadda ta kai kwata fainals, duk da ba a fara wasa dashi a cikin fili.
"Na ji daɗin da na koma West Ham, kuma na kagu na fara taka leda tare da ƴan ƙwallon kungiyar," in ji Fullkrug.
"Ina ganin gasar firimiya ita ce mafi kyau da daraja a duniya, kuma a gare ni lokaci ya yi da zan koma Ingila in buga wasa a babbar ƙungiya, West Ham."
"Na dade ina tunanin West Ham - Na san daraktanta, Tim Steidten sosai, saboda mun kafa tarihi a Werder Bremen tare, kuma na kalli wasu wasannin, na ga irin inganci kungiyar."
Tun a makon jiya Dortmund ta sanar cewar ta amince Fullkrug ya bar sansanin da take buga wasannin sada zumunta a Switzerland, domin ya je ya gana da wata kungiyar.
West Ham ta shiga kasuwa ne, domin sayen mai cin kwallo, wadda take kuma tattaunawa da dan wasan Aston Villa dan kasar Colombia Jhon Duran.
Tuni sabon kociya, Julen Lopetegui ya dauki 'yan wasa da suka hada da Max Kilman daga Wolves kan £40m da mai tsaron raga Wes Foderingham daga Sheffield United da dan Brazil, Luis Guilherme kan £25.5 daga Palmeiras.
Haka kuma West Ham tana son sayen Aaron Wan-Bissaka daga Manchester United da dan kwallon Leeds United, Crysencio Summerville.