Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Man United za ta ɗauki Sterling daga Chelsea
Manchester United na tattaunawa da mahukuntan Chelsea, domin ɗaukar ɗan wasan tawagar Ingila, Raheem Sterling.
Mai shekara 29 na yin atisaye shi kaɗai a Chelsea, bayan da Enzo Maresca ya sanar da shi cewar baya cikin ƴan wasan da zai yi amfani da shi a ƙungiyar.
Har yanzu ba a kai ga cimma matsaya ba, amma dai United na fatan yin amfani da wannan damar domin ta ɗauki ɗan ƙwallo a araha cikin sauki.
United ta ce ita ce za ta taya ɗan wasan, koda yake wasu rahotannin na cewar Chelsea tana sha'awar ɗaukar Jadon Sancho, kenan watakila su yi musaya.
Juventus tana son yin zawarcin Sancho, sai dai United ta ce za ta iya bayar da aron ɗan wasan da yarjejeniyar sayar da shi daga baya, amma ba za ta biya albashinsa a lokacin wasannin aro ba.
Sterling ya yi wa Chelsea karawa 82, wanda ya taka leda a Liverpool da Manchester City, inda ya lashe manyan kofi 10 a Etihad.
Daga nan Chelsea ta ɗauke shi kan yarjejeniyar kaka biyu kan £50m.
A kakar da ta wuce Sancho ya buga wasannin aro a Borussia Dortmund, wanda ya bayar da gudunmuwar da ƙungiyar ta kai wasan karshe a Champions League.