'Yar shekara 12 da ta buɗe aji don koyar da yara a Katsina

Bayanan bidiyo, Latsa alamar da ke sama domin kallo
'Yar shekara 12 da ta buɗe aji don koyar da yara a Katsina
An wallafa

A birnin Katsina, wata yarinya, Khadija Sani Liti 'Yan Kwani, tana cike wani giɓi.

Bayan ta taso daga makaranta, tana zuwa ajin nan, don koyar da Ingilishi ga takwarorinta ƙananan yara. Akwai miliyoyin ƙananan yara da ke buƙatar irin wannan tallafi da zai taimaka musu, su inganta fahimtar darussansu na makaranta. Ƙasashe dai na neman hanyar cimma daidaito da karya lagon fatara da ke sanya wa ana barin miliyoyin yara a baya.

Duk da yake tana karatu ne a aji biyu na ƙaramar sakandire da burin zama masaniyar kimiyyar nukiliya wato nuclear scientist amma kishin ganin ƙannenta su ma sun bunƙasa ya sa Khadija Sani ɗaukar alli don ganin sun samu ilmi mai inganci.

Ma'aikata:

Rahoto: Rabi'atu Runka

Tsara bidiyo: Abba Auwalu