Onana na sha'awar zama a United, Inter da Napoli na hamayya kan Hojlund

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Golan Manchester United Andre Onana, mai shekara 29, yana son ya ci gaba da zama a filin wasan Old Trafford duk da cewa Monaco na zawarcin ɗan wasan na Kamaru. (Guardian)

Zakarun Italiya Napoli sun bi sahun Inter Milan wajen zawarcin ɗan wasan gaban Manchester United Rasmus Hojlund, mai shekara 22, wanda Ruben Amorim ke shirin sanyawa a kasuwa. (Gazzetta Dello Sport)

Dan wasan baya na Crystal Palace Marc Guehi, mai shekara 24, ya shirya tsaf don ƙasrasa shekara ta karshe ta kwantiraginsa idan har dan wasan baya bai samu tayin da ya kwanta masa a rai ba, duk da cewa Liverpool na zawarcin ɗan wasan bayan Ingila. (Guardian)

Arsenal ta fuskanci cikas a yunƙurinta na ɗaukar ɗan wasan gaban Real Madrid Rodrygo, mai shekara 24, inda ɗan wasan na Brazil ke neman albashin fam miliyan 10.2 duk shekara. (AS)

Kulob ɗin Al-Hilal na Saudiyya ya nemi ɗan wasan Napoli Scott McTominay, mai shekara 28, amma ƙungiyar ta Seria A ba ta ma tattauna batun ba saboda ba ta da niyyar rabuwa da ɗan wasan na Scotland. (Football Italia)

Chelsea na shirin sayar da ɗan wasan gaban Senegal Nicolas Jackson, mai shekara 24, a daidai lokacin da ƙungiyoyin Italiya Juventus da Napoli ke zawarcinsa. (Gianluca Di Marzio)

Har yanzu Bayern Munich ba ta fidda rai kan ɗaukar ɗan wasan Sifaniya Nico Williams, mai shekara 22, daga Athletic Bilbao ba, duk da yarjejeniyar da aka cimma tsakanin ɗan wasan da Barcelona. (Mundo Deportivo)

Ɗan wasan gaban Manchester United Marcus Rashford, mai shekara 27, komawa Barcelona duk da cewa kulob ɗin na gab da ɗaukar Williams. (Times)

Paris St-Germain na ci gaba da tattaunawa da ɗan wasan bayan Ukraine Illia Zabarnyi mai shekara 22 daga Bournemouth. (L'Equipe)

Ɗan wasan Manchester United da Ingila Jadon Sancho, mai shekara 25, yana ba da fifikon komawa Napoli a madadin Juventus. (Sky Sports Italia)

Buƙatar Arsenal na ƙara ƙarfin tsakiyarta na iya sa ƙungiyar ta arewacin Landan ta yi zawarcin ɗan wasan Brentford ɗan ƙasar Denmark Christian Norgaard mai shekara 31. (Mirror)