Napoli na son Maguire, ƙungiyoyin Premier na gogayya kan Kolo Muani

Harry Maguire

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Napoli na sha'awar ɗaukar ɗan wasan bayan Manchester United da Ingila Harry Maguire, yayin da Galatasaray ma ta sanya ido kan halin da ɗan wasan mai shekaru 31 ya ke ciki a Old Trafford. (Athletic)

Ɗan wasan gaba na Paris St-Germain Randal Kolo Muani, mai shekara 26, na iya barin ƙungiyar ta Ligue 1 a watan Janairu, yayin da ƙungiyoyin Premier da dama ke sha'awar ɗan wasan na Faransa (Florian Plettenberg)

Dan wasan gaban Chelsea, Christopher Nkunku, mai shekara 27, ya shirya tafiya a watan Janairu sakamakon rashin buga wasa, inda Paris St-Germain da Fenerbahce da Galatasaray ke nuna sha'awa kan ɗan wasan na Faransa. (TBR Football)

Tottenham na shirin miƙa tayin £20m kan golan Burnley da tawagar Ingila ta ƴan ƙasa da shekara 21 James Trafford, mai shekara 22, (Mirror)

Manchester United ta shirya fafatawa da Arsenal domin ɗaukar ɗan wasan Juventus da Serbia Dusan Vlahovic, mai shekara 24. (Football Insider)

Barcelona da Tottenham da Manchester United da Chelsea duk suna zawarcin ɗan wasan Bayern Munich da Jamus Leroy Sane, mai shekara 28. (Sport)

Ipswich Town da West Ham United suna sha'awar komawa da ɗan wasan Galatasaray da Morocco Hakim Ziyech, mai shekara 31, zuwa gasar Premier. (Fichajes)

Tottenham na zawarcin ɗan wasan Borussia Dortmund da Jamus Julian Brandt, mai shekara 28. (Football Transfers)

Arsenal na ci gaba da tattaunawa don sayen ɗan wasan gaba na Sporting CP da Sweden Viktor Gyokeres, mai shekara 26, ko da yake babban burin kulob ɗin a halin yanzu shi ne ɗan wasan RB Leipzig da Slovenia Benjamin Sesko. (Football Transfers)

Crystal Palace na ƙoƙarin ƙulla yarjejeniyar ɗaukar ɗan wasan Jamus Jan-Niklas Beste, mai shekara 25, daga Benfica. (Sacha Tavolieri)

Kocin Juventus Thiago Motta ya buƙaci kulob ɗin na Italiya ya ɗauko ɗan wasan gaban Netherlands Joshua Zirkzee, mai shekara 23, daga Manchester United a watan Janairu. (Sportmediaset)

Kocin Barcelona Hansi Flick ba ya son kulob ɗin ya ɗauki ɗan wasan gaban Manchester United Alejandro Garnacho, mai shekara 20, bayan an yi masa tayin ɗan wasan na ƙasar Argentina.(El Nacional)

Chelsea na shirin miƙa tayin ɗaukar ɗan wasan tsakiyar Faransa Youssouf Fofana, mai shekara 25, daga AC Milan. (Fichajes)