Jami’an Amurka sun tura bayanan sirrin yaƙin Yemen ga ɗanjarida

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

An sanya wani fitaccen ɗanjaridar Amurka a cikin wani dandalin manhajar sada zumunta a bisa kuskure, inda aka riƙa tura bayanan sirri na dakarun soji.

Babban editan mujallar The Atlantic, Jeffrey Goldberg, ya ce bayan Sanya shi cikin dandalin, ya ga bayanan da sakataren tsaron Amurka Pete Hegseth ya tura a ciki game da yadda ƙasar za ta kai hari kan mayaƙan Houthi na Yemen.

Wannan batu dai ya janyo martani da sharhi daga ɓangarori daban-daban, ciki harda na fadar White House.

Shugaba Trump ya ce baya da masaniya a kai, amma ko kaɗan baya da shakku game da tawagarsa ta tsaron ƙasa.

Sakataren tsaron Amurkan Pete Hegseth ya bayyana ɗanjaridar a matsayin mayaudari kuma wanda ya aikata ba daidai ba.

Kakakin majalisar wakilan Amurka, Mike Johnson, wanda ɗan jam'iyyar Republican ne ya bayyana matakin da za a ɗauka.

Ya ce "Gwamnatin tana shawo kan lamarin. Ko shakka babu wata lambar waya da ba a yi niyyar sanya wa cikin dandalin ba, ta samu shiga. Za a gudanar da bincike da kuma tabbatar da cewa ba a sake samun irin haka ba. Amma tattaunawar da aka yi cikin sirri, wadda ta fito fili, ko tantama babu, jami'an gwamnati ne ƙwararru suke aiwatar da ayyukan su cikin ƙwarewa. Kuma na yi nasara a aikin.''

''Muna murna cewa an yi nasarar zartar da abinda aka tattauna ba tare da wani ya kawo tangarɗa ba. A zahiri, ina zaton gwamnati ta yarda cewa an tafka kuskure kuma za su tashi tsaye domin ganin hakan ba ta sake faruwa ba. Babu wani abu da za mu iya ƙara cewa a kai.'' In ji Mr Johnson.

Tuni dai fadar White House ta amsa cewa an tafka kuskuren tura bayanan tsaro na sirri ga ɗanjaridan.

Wannan batu dai ya bayar da mamaki, kuma masu nazari na ganin cewa zai iya dusashe nasarar da Amurkan ta samu a harin da ta kai Yemen, da kuma janyo muhawara a kan ingancin tsarin ɓoye bayanan sirri tsakanin jami'an gwamnati.