Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Pereira ya amince ya zama sabon kocin Wolves
Vitor Pereira ya amince da yarjejeniyar zama kocin Wolves tsawon wata 18.
Kulob ɗin da ke fama a gasar Premier Ingila ta bana zai biya kusan yuro miliyan ɗaya domin ɗaukar kocin daga ƙungiyar Al-Shabab ta Saudiyya.
Ɗan ƙasar Portugal ɗin kuma tsohon kocin FC Porto da Olympiakos, zai je Ingila ranar Talata, kodayake dai bai sanya hannu kan wata yarjejeniya ba tukunna.
Wasan farko da mai shekara 56 ɗin zai ja ragama shi ne wanda za su fafata da Leicester City ranar Asabar, inda Wolves ke mataki na biyun ƙarshe a teburin gasar.
Wolves ta yi rashin nasara a wasa 11 na Premier bana cikin 16 da ta buga.
Ta kori mai horaswa Gary O'Nell ne a ranar Lahadi bayan kashin da ta sha 2-1 a hannun Ipswitch, wadda ita ma ke fama.
Pereira ya koma Al-Shabab a watan Fabrairu, inda suka ƙare a mataki na takwas a teburin gasar Saudi Pro League da ta gabata. Yanzu suna mataki na shida bayan cin wasa bakwai cikin 13 da suka buga.