Shugabannin Amurka da aka kashe tun daga Abraham Lincoln

Abraham Lincoln ne shugaban Amurka na farko da aka harbe yana kan mulki

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Abraham Lincoln ne shugaban Amurka na farko da aka harbe yana kan mulki
An wallafa
Lokacin karatu: Minti 5

An kawo karshen gagarumin neman mutumin da ya harbe Charlie Kirk, mai tsattsauran ra'ayin rikau da kishin farar fata kuma abokin siyasar Shugaban Amurka Donald Trump.

Jami'an tsaro a Amurkar suna tsare da mutumin da ake zargi da kashe Kirki, kwanaki biyu bayan kaddamar da nemanshi.

Jami'ai sun ce an mika musu matashin mai suna Tyler Robinson mai shekara 22, bayan ya amsa da bakinsa shi ya aikata kisan.

Kafafen yada labaran Amurka sun ce mahaifinsa ne ya fara tararsa da batun bayan 'yan sanda sun yada hotunansa.

Kirk mai ra'ayin riƙau na jawabi ne a wata jami'a da ke jihar Utah ranar Laraba lokacin da ɗanbindigar ya harbe shi a wuya sau ɗaya, kuma aka tabbatar da mutuwarsa jim kaɗan bayan haka.

Gwamnan jihar da Trump sun alaƙanta kisan da jagaliyar siyasa.

Harbin na Kirk ƙari ne kan abubuwan da aka taɓa gani a siyasar Amurka, waɗanda suka shafi fitina a siyasance.

Mun duba wasu daga cikin manyan 'yansiyasa da aka yi wa kisan gilla a tarihin Amurka.

Shugabannin ƙasa

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Abraham Lincoln, shugaban ƙasa na 16

Lincoln ne shugaban ƙasar Amurka na farko da aka kashe: John Wilkes Booth ne ya harbe shi ranar 14 ga watan Afirilun 1865 yayin da suke halartar wani biki tare da matarsa a birnin Washington DC.

Lincoln ya mutu kwana ɗaya bayan haka. An ce goyon bayan da yake nunawa game da 'yancin baƙar fata ne ya jawo kisan nasa.

Daga baya aka kashe Booth shi ma a Virginia.

James Garfield, shugaban ƙasa na 20

Garfield ne shugaban Amuka na biyu da aka yi wa kisan gilla. Yana tafiya a tashar jirgin ƙasa ta birnin Washington DC ranar 2 ga watan Yulin 1881 lokacin da Charles Guiteau ya harbe shi.

Ya mutu a watan Satumba na shekarar bayan likitoci sun kasa gano harsashin da ke jikinsa.

Guiteau da aka ce yana da taɓin hankali, an kama shi da laifin kisan kuma aka zartar masa da hukuncin kisa a watan Yunin 1882.

William McKinley, shugaban ƙasa na 25

An harbe McKinley lokacin da yake jawabi a Buffalo da ke birnin New York ranar 6 ga watan Satumba na 1901, kuma ya mutu 'yan kwanaki bayan haka sakamakon illar da harsashin ya yi masa.

Wani mai suna Leon Czolgosz ne ya harbe shi. An kama shi da laifin tare da zartar masa da hukuncin kisa a watan Oktoban 1901.

Shugaban Amurka John F Kennedy, da Uwargidansa Jacqueline Kennedy, da Gwamnan Texas John Connally, da sauran mutane na yi wa jama'a murmushi daga cikin mota a Dallas ranar 22 ga watan Nuwamban 1963. 'Yan mintuna bayan haka ne kuma aka harbe shugaban.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Kisan gillar da aka yi wa Shugaba JFK har yanzu na cikin lamurran da suka gagari hukumomin Amurka

John F Kennedy, shugaban ƙasa na 35

An harbe Kennedy da wata bindiga mai ƙarfi lokacin da yake ziyara a Dallas ranar 22 ga watan Nuwamban 1963. An ji ƙarar harbe-harben ne yayin da ayarin motocin shugaban ke wucewa.

An garzaya da Kennedy asibiti, inda ya mutu jim kaɗan bayan haka.

Sa'o'i bayan haka ne kuma 'yansanda suka kama Lee Harvey Oswald, wani tsohon soja. Kwana biyu bayan haka, sai mai gidan rawa a Dallas Jack Ruby ya harbe shi yayin da ake sauya masa gidan yari.

Ɗantakarar shugaban ƙasa

Robert F Kennedy, sanata na jam'iyyar Democratic

Robert F Kennedy tsohon sanata ne daga New York kuma ɗan'uwan John F Kennedy, wanda aka kashe shekara biyar kafin lokacin.

Kennedy na neman tsayawa takarar shugaban ƙasa a jam'iyyar Democrat lokacin a aka kashe shi a wani otal da ke Los Angeles, 'yan sa'o'i bayan ya gama yin jawabin nasara a zaɓen fitar da gwani na jihar California.

An kama maharbin Sirhan Sirhan da laifin kisa kuma aka ɗaure shi rai-da-rai.

'Yan gwagwarmaya

Ɗan gwagwarmayar kare haƙƙi a Amurka Martin Luther King Jr kenan yake ɗaga wa mutane hannu ranar 28 ga watan Agustan 1963 a Washington DC yayin jawabin "I Have a Dream".

Asalin hoton, AFP via Getty Images

Bayanan hoto, Kisan Martin Luther King Jr ya girgiza Amurkawa a lokacin kuma har yanzu ana yi masa kallon babban lamari a tarihin ƙasar

Martin Luther King Jr

An kashe ɗan gwagwarmayar 'yancin baƙaƙen fata Dr Martin Luther King Jr a Memphis, jihar Tennessee a 1968, inda yake shirin jagorantar wani gangami na ma'aikata game da ƙarancin albashi.

Wani ɗanbindigar ƙin jinin baƙar fata ne James Earl Ray ya harbe shi lokacin da yake tsaye a farfadiyar wani otal. Ya mutu a asibiti jim kaɗan bayan haka yana da shekara 39.

Dr King ya sha tsallake rijiya da baya a yunƙurin kashe shi, ciki har da harin bam a kan gidansa a 1956.

Malcolm X

Malcolm X, mai fafutikar kare haƙƙin baƙar fata, an harbe shi a New York City a kan idon iyalinsa a 1965.

An kashe shi yana da shekara 39.

Ya daɗe yana magana da yawun ƙungiyar Nation of Islam, wadda ta yi ta neman 'yancin baƙar fata masu tsaurin ra'ayi, amma daga baya ya sassauta ra'ayinsa.

An kama Muhammad Aziz, da Khalil Islam, da Thomas Hagan da laifin kisan kuma aka ɗaure su rai-da-rai. A 2021 kuma wata babbar kotu ta wanke Aziz da Islam.

Malcolm X kenan yake fitowa daga mota a kofar gidansa da aka kai wa harin bam

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, An kai wa gidan Malcolm X harin bam mako ɗaya kafin kashe shi

Yunƙurin kisa na baya-bayan nan

A baya-bayan nan, a watan Yuni aka kashe wasu 'yanmajalisar jiha na jam'iyyar Democrat a Minnesota.

An harbe Melissa Hortman da mijinta Mark a gidansu.

Sai dai Sanata John Hoffman da matarsa Yvette da aka harba da harsasai da yawa sun tsallake rijiya da baya.

An harbi Donald Trump a kunne lokacin da aka yi yunƙurin kashe shi a 2024

Asalin hoton, AFP via Getty Images

Bayanan hoto, An harbi Donald Trump a kunne lokacin da aka yi yunƙurin kashe shi a 2024

A shekarar da ta gabata kuma aka yi yunƙurin kashe Donald Trump har sau biyu.

A watan Yulin 2024, harsashi ya gogi kunnensa yayin wani yaƙin neman zaɓe a Butler, Pennsylvania, wanda ya yi kama da harbin da aka yi wa Charlie a Utah.

A watan Satumban shekarar kuma, jami'an tsaro suka ce sun daƙile wani yunƙurin kisan Trump ɗin a filin wasan Golf nasa da ke Florida.

Shekara biyu kafin haka, wani mai riƙe da guduma ya ɓalla gidan shugabar majalisar wakilai ta lokacin Nancy Pelosi 'yar Democrat.