Arsenal ta kammala ɗaukar Merino daga Real Sociedad

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Arsenal ta kammala ɗaukar ɗan wasan tawagar Sifaniya, Mikel Merino daga Real Sociedad kan £31.6m.

Mai shekara 28 ya koma Gunners kan kwantiragin kaka huɗu da cewar za a kara masa wata 12 idan ya taka rawar gani.

Tun farkon kuɗin cinikin ya kama kan £27.4m da karin tsarabe-tsaben £4.2m ga ɗan wasan.

Merino yana cikin tawagar Sifaniya da ta lashe Euro 2024 a Jamus, ya kuma buga dukkan wasa bakwai da cin Jamus ƙwallo a zagayen kwata fainal.

Mai shekara 28 yana da sauran ƙunshin kwantiragin da bai kai kaka daya ba a Real Sociedad mai buga La Liga.

Merino shi ne na uku da Gunners ta ɗauka a bana, bayan ɗan kasar Italiya, Riccardo Calafiori da golan Sifaniya, David Raya, wanda ya buga mata wasannin aro a bara daga Brentford.

Daukar Merino da Arsenal ta yi zai bai wa Mikel Arteta karin masu buga gurbin tsakiya da ya haɗa da Declan Rice da Jorginho da Thomas Partey da kuma Martin Odegaard.

Merino ya kwan da sanin gasar Premier League, wanda ya yi kaka ɗaya a Newcastle daga nan ya koma Real Sociedad a 2018.

A Sifaniya ya taka leda tare da Odegaard a 2019-20 a Real Sociedad, lokacin da ya buga wasannin aro daga Real Madrid.

Merino, ya buga wa Sifaniya wasa 28, wanda ya yi karawa 45 a dukkan fafatawa a bara da cin ƙwallo takwas.