Alhilal ta lasa wa Fernandes zuma, Wirtz ya gwammace ya koma Liverpool kan Munich

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 3

Al Hilal na shirin bayar da fan miliyan 100 don daukar Bruno Fernandes daga Manchester United, Florian Wirtz ya fi son ya koma Liverpool a kan Bayern Munich, yayin da Emiliano Martinez ke shirin barin Aston Villa.

Za a ba Kyaftin din Manchester United Bruno Fernandes wa'adin mako mai zuwa don yanke shawarar ko yana son barin kulob din, inda Al Hilal ke tayin kusan fan miliyan 100 kan dan wasan na Portugal, mai shekara 30, wanda zai rika samun kusan fan miliyan 65 a shekara a Saudiyya. (Mail)

Bayern Munich na iya sake yin wani sabon yunkuri don daukar Fernandes din duk da cewa kudin da United ke so sun mata yawa. (Teamtalk)

Dan wasan gefe na Argentina Alejandro Garnacho, mai shekara 20, na iya barin Manchester United a wannan bazarar bayan da ya ji takaicin rawar da yake takawa a karkashin kocin kungiyar Ruben Amorim. (ESPN)

Wakilan Garnacho na shirin tattaunawa da Manchester United domin tattauna makomar dan wasan na Argentina bayan da aka yi watsi da shi a wasan karshe na gasar cin kofin Europa da Tottenham ta yi. (Telegraph)

Ita ma Manchester United da alama za ta siyar da dan wasan tsakiyar Ingila Kobbie Mainoo, mai shekara 20, a wani yunkuri na rage matsin lamba a kungiyar. (Sun)

Dan wasan tsakiyar Jamus Florian Wirtz, mai shekara 22, zai gwammace ya koma Liverpool maimakon Bayern Munich idan ya bar Bayer Leverkusen a bazara. (Athletic)

Bayern Munich ta yi imanin dan wasan Brighton da Japan Kaoru Mitoma, mai shekara 28, zai iya zama madadin Wirtz. (Sky Germany)

Everton ta tattauna da dan wasan Ipswich da Ingila na 'yan kasa da shekara 21 Liam Delap, mai shekara 22, kan komawa kungiyar a bazara kuma suna sha'awar dan wasan Liverpool da Scotland Ben Doak, mai shekara 19. (Guardian)

Real Madrid na kallon dan wasan Liverpool da Argentina Alexis Mac Allister a matsayin wanda zai maye gurbin dan kasar Croatia Luka Modric, mai shekara 39, wanda zai bar Bernabeu a bana. (Fichajes)

RB Leipzig ta tuntubi sabon daraktan wasanni na Arsenal Andrea Berta game da yiwuwar siyar da dan wasan gaban Slovenia Benjamin Sesko mai shekaru 21. (Sky Sports Germany)

Har yanzu kofar dan wasan Wolves da Brazil Matheus Cunha, mai shekara 25, a bude take, don komawa Manchester United a bazara duk da rashin samun gurbin shiga gasar cin kofin Turai a kakar wasa mai zuwa. (Sky Sports)

Golan Aston Villa Emiliano Martinez, mai shekara 32 na shirin barin kungiyar, inda kungiyoyin Saudiyya da Manchester United ke zawarcin dan wasan na Argentina. (Teamtalk)

Aston Villa, da West Ham da Leeds suna zawarcin dan wasan tsakiya na Southampton da Portugal na 'yan kasa da shekara 21 Matheus Fernandes, mai shekara 20. (Football Insider).