Darussa biyar da ya kamata a ɗauka daga zaɓen cike gurbi a Najeriya

Asalin hoton, Inec
A zaɓukan cike gurbin da aka yi a Najeriya a ƙarshen mako, ana ganin sakamakon sun zo da ba-zata, musamman ganin yadda duk da irin rawar ganin da babbar jam'iyya mai mulkin a ƙasar ta taka, wasu jam'iyyu sun samu nasara a jihohin da suke mulki.
An gudanar da zaɓukan ne domin maye gurbin zaɓaɓɓu 16 a sassa daban-daban na jihohin ƙasar 12, inda APC ta lashe mafi yawan kujeru.
Babban abin da ya ɗauki hankali a zaɓen shi ne irin rawar jam'iyyar ADC ta haɗakar manyan ƴansiyasar adawa ta ƙasar ta taka, inda wasu suka yi tunanin ba ta yi takaɓus ba a lokacin da ya kamata ta nuna ƙwanji.
Sai dai a wata sanarwa da kakakin jam'iyyar, Bolaji Abdullahi ya fitar, ya ce ko kaɗan bai kamata a fara kwatanta ƙoƙarinsu da abin da ya faru a zaɓen ba, domin a cewarsa, yanzu suka fara shiri.
A wani ɓangaren kuma, masu bibiyar harkokin siyasar ƙasar suna tafka muhawara kan irin nasarar da APC ta samu a daidai lokacin da wasu ƴan ƙasar ke ƙorafin irin halin da ake ciki na tsadar da rayuwa.
Wannan ya sa muka kalato wasu muhimman darussa da za a iya koya daga zaɓukan.
Rawar da ADC ta taka
Ganin irin rawar da jam'iyyar ADC ta taka a zaɓen, sai wasu ke cewa duk da jigi-jigan da jam'iyar ta tara, ta kasa lashe kujera ko ɗaya.
Amma a nasa hangen, Dokta Kabiru Sufi, masanin kimiyyar siyasa kuma malami a kwalejin share fagen shiga jami'a a Kano, ya ce yana ganin ta taka rawar gani duk da rashin lashe kujerar.
"Akwai wuraren da ta yi ƙoƙari har da ta ta uku, musamman a jihohin da aka fafata tsakanin jam'iyya mai mulki a tarayya da mai mulki a jiha. Don haka ina ganin za a iya cewa ta fara da ƙafar dama, kuma ta samu tagomashi."
Sai dai ya ce akwai buƙatar jam'iyyar ta buɗe ido daga wannan zaɓen wajen nuna wa jama'a cewa lallai ita ce jam'iyyar haɗakar.
Tun da farko dai, an ga yadda tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-rufai ya dage kai da fata wajen yaƙin neman zaɓen cike gurbin, sannan tsohon ɗantakarar Jam'iyyar Labour ya yi kira ga magoya bayansa da su zaɓi ADC a zaɓukan.
A game da yadda duk da haka jam'iyyar ba ta samu nasara ba, Sufi ya ce dama zaɓukan ciken gurbin ya fi zafi ne a tsakanin jam'iyya mai mulki a ƙasa da mai mulki a jiha idan daban ne.
Gwamnoni ke da wuƙa da nama
Daga cikin abin da ya ja hankali a zaɓukan, shi ne irin yadda gwamnonin jiha suka taka rawar gani wajen nasarar ƴantakarar da suke so, wanda hakan ya sa wasu suke ganin tamkar su ne suke riƙa da wuƙa da nama a zaɓukan jihohin su.
Shi ma Dr Sufi ya aminta da wannan ra'ayin, inda ya ce, "zaɓen ya sake haska cewa gwamnoni da dama suna da damarmaki a hannunsu da suke amfani da su wajen cin zaɓe," in ji shi.
Masanin harkokin siyasar ya ƙara da cewa gwamnoni suna amfani da masu riƙe da madafun ikon da suke jihar, "inda za ka ga gwamna ya tura kwamishinoni da shugabannin ƙananan hukumomi da kansiloli zuwa wuraren zaɓe su taru domin ganin sun samu nasara."
A game da tasirin da gwamnonin za su iya yi a babban zaɓe mai zuwa, Sufi ya ce "babban zaɓe gama-gari ne, ba su tara ƙarfinsu a waje guda ba, amma akwai yiwuwar su yi tasiri kamar yadda aka saba gani, ko ma ya wuce haka."
APC ta samu gagarumar nasara
A wani ɓangaren kuma, irin nasarar da APC ta samu a zaɓen ya zo da ba-zata, ganin a wasu ƴan ƙasar na bayyana rashin jin daɗin wasu matakan gwamnati, waɗanda suka cewa sun jawo tsadar rayuwa a ƙasar.
A game da wannan, Kabiru Sufi ya ce ba ya rasa nasaba da kasancewar ita ce take mulki a yanzu.
"Tana amfani da masu riƙe da madafun iko, waɗanda su kansu kowa ke ƙoƙarin ganin ya taɓuka wani abu. Ina ganin har yanzu ƴan ƙasa ba sa iya bambancewa tsakanin abin da jam'iyya ta yi, da wanda ba jam'iyyar ba ce. Za ka suna ƙorafi, amma idan an zo zaɓe, sai su yi akasin abin da suke faɗa."
"Amma lallai haƙiƙanin abin da ke faruwa a Najeriya shi ne jam'iyyu masu tasiri su ne suke cigaba da zama masu tasirin, marasa tasiri ko da sun fitar da ƴantakara masu inganci suna rasa kataɓus."
Neman nasara da ƙarfi da yaji
A lokacin zaɓen, rudunar ƴansandan jihar Kano ta ce ta kama mutum 288 da ta ce ƴan daba ne da take zargi da tayar da hargitsi a wajen zaɓen.
Haka lamarin ya faru a wasu jihohin, inda aka kama wasu mutanen, sannan an kama wasu mutane da maƙudan kuɗaɗe a hannunsu, wanda aka yi zargin sayen ƙuri'a suke yunƙurin yi.
A game da yadda dabanci ke tasiri a zaɓe, Dokta Kabiru Sufi ya ce dukkan ɓangarorin da suka shiga zaɓen sun yi amfani da ƴandaba, waɗanda a cewarsa suna barazana ga dimokuraɗiyyar ƙasar.
"Tun lokacin yaƙin zaɓe aka fara shiga fargaba saboda irin kalaman da suka riƙa fitowa, kuma da zaɓen ya zo sai aka riƙa ganin abin da suka faɗa na fitowa. A wasu wuraren har ƴanjarida da ƴansanda an kai musu hari."
Sufi ya ce harkar dabanci na matuƙar barazana ga siyasar Najeriya, "suna hanawa a gudanar da sahihin zaɓe, sannan bayan zaɓe su koma cikin al'umma."
INEC: Ba yabo ba fallasa

Asalin hoton, Getty Images
A duk lokacin da zaɓe ya zo, a kan mayar da hankali kan irin rawar da hukumar zaɓe za ta taka wajen samun nasarar gudanar da zaɓe sahihi, inda ƴan ƙasa suke fata ta zama ƴar tsakiya ba tare da nuna ɓangaranci ba.
A wannan zaɓen na cike gurbi, jam'iyyu masu mulki a wasu jihohi sun samu nasara, duk kuwa da cewa ba ita ce jam'iyya mai mulki a ƙasar, wannan ya sa wasu ke ganin ya kamata a yaba mata.
Dokta Kabiru Sufi ya ce babu yabo babu fallasa a game da irin rawar da INEC ta taka a zaɓen.
"A zaɓen an samu inda zaɓen bai kammalu ba, sannan akwai wuraren da aka samu rashin gamsuwa. Misali a Kano, dukkan jam'iyyun sun ce ba su gamsu da zaɓen kujerar da ba su samu nasara ba. Wannan ya nuna cewa akwai sauran ƙalubale a gaban INEC," in ji masani siyasar.
Sakamakon zaɓen da aka yi ya nuna cewa APC ta samu nasara a kujera 12 cikin 16 da aka fafata, amma ADC ba ta lashe ko ɗaya ba.
An ga yadda tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya dage wajen yaƙin neman zaɓe, da kuma sanarwar da Peter Obi ya fitar, wadda a ciki ya buƙaci magoya bayansa su zaɓi ADC a zaɓen.
Sai dai APGA ta lashe kujera byu, NNPP ta lashe ɗaya, PDP ta lashe ɗaya, sannan INEC ta ce zaɓen Ƙaura-Namoda bai kammalu ba.
A Adamawa, APC ta lashe kujerar majalisar jiha ta Ganye, duk da cewa gwamnan jihar, Ahmadu Fintiri ɗan PDP ne.
A Anambra, APGA ta ƙara samun tagomashi wajen lashe zaɓen sanatan Anambra ta Kudu, sannan a Oyo PDP ce ta lashe zaɓen majalisar wakilai ta Ibadan ta Arewa, haka kuma NNPP ta lashe kujerar Bagwai/Shanono a Kano.
A Taraba, APC ce ta lashe zaɓen majalisar jiha ta Karim I, duk da gwamnan jihar ɗan PDP ne.











