Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Van Dijk ya buga wasa na 100 a Premier a Anfield ranar Lahadi
Virgil van Dijk ya buga wasa na 100 a Premier League a Anfield ranar Lahadi, inda Liverpool ta doke Brentford 2-0 a wasan mako na biyu a gasar.
Cikin wasannin an yi nasara 82 da shi a babbar gasar tamaula ta Ingila a gida da canjaras 16, yayin da aka yi rashin nasara da ci a karawa biyu.
Wasan da aka ci Liverpool a Anfield da Van Dijk a cikin fafatawar a Premier League shi ne wanda Leeds United ta ci 2-0 a kakar 2022/23.
Ɗaya wasan kuwa shi ne wanda Crystal Palcce ta yi nasara a Anfield a bara, ɗaya daga karawar da ta bai wa Liverpool matsalar lashe Premier a kakar da ta wuce.
Ƙyaftin ɗin tawagar Netherlands ya samu maki 262 a wasa 100 a Premier League a Anfield, wanda ke gabansa shi ne Patrice Evra mai maki 263 a Manchester United a Old Trafford.
Van Dijk tsohon ɗan wasan FC Groningen da Celtic da Southampton ya koma Liverpool ranar 1 ga watan Janairun 2018, kwantiraginsa zai kare a karshen kakar nan a Anfield.
Luis Diaz da Mohamed Salah ne suka ci wa Liverpool ƙwallayen da ya ba ta maki ukun da take bukata a Anfield a kan Brentford.
Liverpool ta fara doke Ipwich Town 2-0 ranar 17 ga watan Agusta a wasan makon farko a Premier League, inda Diogo Jota da Mohamed Salah suka ci mata ƙwallayen.
Kenan Liverpool, wadda har yanzu ba ta ɗauki ɗan wasa ba a bana ta ci wasa biyu a jere da zura kwallo hudu ba tare da ko ɗaya ya shiga ragarta ba a Premier ta bana.
Haka kuma a karon farko Liverpool ta buga wasa a Anfield ba tare da Jurgen Klopp ba, bayan shekara tara, wanda ya yi murabus a karshen kakar da ta wuce.
Tuni kuma ƙungiyar ta naɗa Arne Slot daga Feyennord, wanda ya maye gurbin Klopp ɗan kasar Jamus.
Ranar Lahadi 1 ga watan Satumba, Liverpool za ta je Manchester United, domin buga wasan mako na uku a Premier League.