Ƴan Real Madrid da suka je Bilbao buga La Liga

Asalin hoton, Getty Images
Athletic Bilbao za ta karɓi bakuncin Real Madrid a wasan mako na 16 a La Liga da zasu kara a San Mames ranar Laraba.
Sun fuskanci juna a bara, inda Real Madrid ta je ta ci 2-0 gida da waje a babbar gasar tamaula ta Sifaniya.
Wasan da aka buga a bara tsakanin Bilbao da Real Madrid
Spanish La Liga Lahadi 31 ga watan Maris 2024
- Real Madrid 2 - 0 Ath Bilbao
Spanish La Liga Asabar 12 ga watan Agusta 2023
- Ath Bilbao 0 - 2 Real Madrid
Real Madrid mai ƙwantan wasa tana ta biyun teburi da maki 33, ita kuwa Bilbao mai maki 26 tana ta huɗun teburin La Liga.
Barcelona ce ta ɗaya da maki 34, bayan da ta je ta caskara Real Mallorca 5-1 ranar Talata, bayan da ta yi karawar mako na 16.
Ƴan wasan Real Madrid da suka je Bilbao:
Masu tsare raga: Courtois, Lunin da Mestre.
Masu tsare baya: Lucas Vázquez, Vallejo, Fran García, Rüdiger, Mendy, Asencio da Lorenzo Aguado.
Masu buga tsakiya: Bellingham, Valverde, Modrić, Tchouameni, Arda Güler da Ceballos.
Masu cin ƙwallaye: Mbappé, Rodrygo, Endrick, Brahim da Gonzalo.











