Messi ya kai Argentina wasan karshe a Kofin Duniya a Qatar

Asalin hoton, Getty Images
Argentina ta kai wasan karshe a Gasar Cin Kofin Duniya da Qatar ke karbar bakunci, bayan da ta casa Croatia da ci 3-0 ranar Talata a filin Lusail.
Messi wadda ke buga Gasar Kofin Duniya ta biyar kuma ta karshe mai shekara 35, shi ne ja ragamar nasarar da Argentina ta yi tare da Alvarez matashi mai shekara 22.
Hakan ya sa Argentina za ta buga wasan karshe ranar Lahadi da duk wadda ta yi nasara a karawar Laraba ta daf da karshe tsakanin Faransa da Morocco.
Messi ne ya fara cin kwallo a bugun fenariti a minti na 34 da fara wasa na 11 a gasar Kofin duniya biyar da ya buga, ya hau kan Gabriel Batistuta, wanda ya ci wa Argentina 10 a kofin duniya a tarihi.
Argentina ta kara na biyu ta hannun Julian Alvarez minti biyar tsakani, wanda ya ci na uku a Qatar, mai taka leda a Manchester City.
Bayan da suka yi hutu suka koma zagaye na biyu ne Argentina ta kara na uku, kuma na biyu ta hannun Alvarez, kuma na hudu da ya zura a raga a Qarar.
Hakan ya sa Argentina ta rama 3-0 da Croatia ta yi mata a Rasha a 2018, gasar da Faransa ta lashe, bayan cin Croatia a karawar karshe da ci 4-2.
Tun farko Argentina ta kai wasan daf da karshe, bayan nasara a kan Netherlands da ci 4-3 a bugun fenariti, bayan da suka tashi 2-2.
Ita kuwa Croatia fitar da Brazil ta yi a bugun daga kai sai mai tsaron raga da ci 4-2, bayan da suka tashi 1-1 har da karin lokaci.
Messi ya kai wasan karshe a 2014, inda Jamus ta yi nasara a kan Argentina ta lashe kofin a Brazil a filin wasa na Maracana.
Karo na shida da Argentina ta kai wasan karshe a babbar Gasar tamaula ta duniya, bayan da ta dauki kofin sau biyu na karshe shi ne a 1986.
Messi ya buga wasa na 25 a Gasar Cin Kofin Duniya ya kuma yi kan-kan-kan da Lutha Matthaus na Jamus mai wannan kwazon a baya.











