Kane ya kafa tarihin cin kwallaye a Bundesliga

An wallafa

Dan wasan tawagar Ingila, Harry Kane na ci gaba da taka rawar gani a Bundesliga a bana, bayan da ya ci Heidenheim kwallo biyu ranar Asabar.

Nasarar da Bayern Munich ta doke Heidenheim 4-2 ya sa ta koma jan ragamar Bundesliga na kakar nan, bayan wasa 11.

Kane tsohon dan wasan Tottenham ya ci kwallo biyu ranar Asabar, kenan ya zura 17 a raga a bana jimilla kawo yanzu.

Bayan da ya ci kwallo uku rigis a baya har karo biyu a Bundesliga, Kane ya kafa tarihin zura kwallaye da yawa a raga a Bundesliga, bayan karawa 11.

Ya wuce tarihin da Robert Lewandowski ya kafa mai kyallo 16 a raga a wasa 11 a Bundesliga a kakar 2019.

Bayern tana ta daya a kan teburin Bundesliga da tazarar maki daya tsakaninta da Bayern Leverkusen, wadda za ta iya karbar gurbinta da zarar ta doke Union Berlin ranar Lahadi.

Kane, wanda ya koma Bayern Munich a bana, tuni ya hau kan wadanda suka fi cin kwallaye a bara a Bundesliga, wato Christopher Nkunku da kuma Niclas Fullkrug masu 16 kowanne.

Wannan shi ne karo na 10 a jere da Kane ke cin kwallo 20 ko fiye da haka a kungiya, kuma 17 da ya zura a raga a Bundesliga ya yi kan-kan-kan da Erling Haaland, wanda ya yi haka a Manchester City a Premier League a bara a karawa 11.