World Cup 2022: Suarez ya ki bai wa Ghana hakuri bayan cire kwallo da hannu a 2010

Suarez

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Dan wasan gaban Uruguay Luis Suarez ya ki ba da hakuri kan kwallon da ya cire da hannu a wasansu da Ghana na gasar kofin duniya ta 2010.

Suarez ya karbi jan kati a mintin karshe na karin lokaci, a zagayen kwata-fayinal, bayan da ya cire kwallo yayin da za ta shiga ragarsu dagangan.

Sai dai dan wasan gaban Ghana Asamoah Gyan ya barar da bugun finareti, wanda a karshe hakan ya bai wa Uruguay damar kai wa zagayen kusa da na karshe.

"Dan wasan Ghana ne ya barar da finareti ba ni ba,” in ji Suarez, kafin haduwar kasashen biyu a rukunin G ranar Juma’a.

Idan har Ghana ta samu nasara za ta kai zagaye na gaba, to amma idan Uruguay ta yi nasara itama za ta kai zagaye na gaba, duk da sai ta jira ta ga cewa Koriya ta Kudu ba ta doke Portugal ba.

Idan kuma har Uruguay da Koriya ta Kudu duka suka ci wasa, yawan kwallaye ne zai raba su, duk da a gabar da ake Koriya ta Kudu ce gaba da kwallo daya.

Wannan ne karon farko da Ghana da Uruguay za su kara da juna tun bayan bakin cikin da Suarez ya saka yan Ghana shekaru 12 da suka wuce.

Kuma tsohon dan wasan gaban Liverpool din ya ce ba ya da-na-sani, duk da wani dan jaridar Ghana ya fada masa cewa yan Ghana na yi masa kallon ‘mugu’.

"Ba zan ba da hakuri kan abunda na yi ba. Ina ba da hakuri ne idan na raunata dan wasa, amma na karbi jan kati kan fitar da kwallon da hannu a lokacin.” In ji Suarez.

Ya kara da cewa “ ba laifi na bane don ba ni na barar da finareti ba.’’

 

Ghana Uruguay

Sai dai abunda Suarez ya yi a 2010 ya haifar masa da mummunar tsana a Ghana, musamman irin salon murnar da ya yi a gaban magoya bayan Ghana bayan da suka yi nasara a bugun finareti.

Daga nan kuma su Suarez sun yi rashin nasara a zagayen kusa da karshe a karawarsu da Netherlands.

To amma tawagar Ghana ta yanzu sun zabi su ba da baya kan batun daukar fansa kan Suarez da Uruguay, inda kyaftin dinsu Andrew Ayew, wanda shi kadai ne daga tawagar ta 2010, yace baya da burin tuna baya illa abunda zai faru gaba.

"Ba wanda ya ji dadin abunda ya faru a 2010, amma ni fata ne shi ne mu kai zagaye na gaba. Ko da ba batun fansa ko babu, za mu je ne da kwarin gwuiwa da kwadayin samun nasara,’’ in ji Ayew.

“Ba na tuna baya, ba na son mayar da hankali kan abunda ya riga ya wuce.”