Muhimmancin azumin Tasu'a da Ashura

Bayanan bidiyo, Sheikh Abdulmajid Muhammad Umar
Muhimmancin azumin Tasu'a da Ashura
An wallafa

A duk ranar 9 da 10 ga watan Muharram na shekarar Musulunci, Musulmi da dama kan yi azumi da ake kira Tasu'a da Ashura da nufin neman gafara.

An dai ce hadisan Annabi sun bayyana falalar azumin na kwana biyu da samun gafarar zunuban shekarar da ta gabata da wadda za ta zo.

Sheikh Abdulmaji Muhammad Umar da ake yi wa lakabi da Almadani kuma malamin addinin Musulunci a Kaduna ya ce azumin yana da asali'

"Lokacin da annabi Muhammad SAW ya yi hijira zuwa Makka ya samu Yahudawan wurin suna azumi a ranar 10 ga watan na Muharram. Sai ya tambaye su dalili sai suka ce suna yi ne domin girmama annabi Musa AS wanda Allah ya tseratar ranar."

Ranar 9 ga wata dai za ta kama Alhamis inda kuma Juma'a za ta kama 10 ga watan na Muharram.

Islamic cleric