An fara shirin raba gari tsakanin Mbappe da PSG

An wallafa

Idan za a yi la'akari da abubuwan da suka faru a wasan ƙarshe da Paris St-Germain ta buga, akwai alamun cewa za a samu abubuwan ban mamaki a ƴan watannin da suka rage wa Kylian Mbappe a kulob ɗin na Faransa.

Mbappe ya amince ya koma Real Madrid a wannan bazarar, kuma duk da cewa PSG ba ta tabbatar da hakan a hukumance ba alamu sun fara nuna cewa ta fara shirin rayuwa ba tare da shi ba.

A karawar da ta yi da Monaco a ranar Juma’ar da ta gabata, inda wasan ya ƙare babu ci, an cire Mbappe ne a lokacin hutun rabin lokaci.

Amma maimakon zama tare da takwarorinsa a bencin PSG, Mbappe ya zabi ya zauna tare da mahaifiyarsa a cikin ƴan kallo.

Yanzu dai an sauya Mbappe a wasanni biyu a jere, inda aka maye gurbinsa bayan mintuna 65 a wasan da suka tashi 1-1 da Rennes bayan ya kasa zura ƙwallo a raga.

"Ko ba-jima ko ba-daɗe sai mun fara sabawa da wasa ba tare da Kylian ba," in ji kocin PSG Luis Enrique bayan wasan. "Dole ne in ɗauki matakin da ya fi dacewa ga ƙungiyar."

Mbappe ya ci wa PSG ƙwallaye 26 a dukkan gasa a kakar wasa ta bana, inda 21 daga cikinsu suka zo a gasar Ligue 1 wanda ya sa ya zama kan gaba a jerin masu cin ƙwallo a gasar.

PSG dai tana kan hanyar kare kambinta na gasar ƙasar Faransa inda ta ke da tazarar maki tara tsakaninta da Brest wadda ke a matsayi na biyu.

Amma yayin da nasarorin cikin gida suka zo cikin sauki ga PSG a ƙarƙashin mallakar ƴan Qatar, samun nasara a gasar zakarun Turai ya faskara.

Idan aka yi la’akari da tarihin bajintarsa a gasar, da alama PSG za ta yi wa kanta sakiyar da babu ruwa idan har ba ta samu abin da ya kamata ba daga shararren ɗan wasan na duniya kafin ya tafi.