Gasar kofin Afirka ta mata: Atisayen Super Falcons a Morocco

An wallafa

Danna hoton da ke sama domin kallon bidiyon:

Tawagar Super Falcons ta Nageriya za ta buga wasan farko da Afirka ta Kudu ranar Litinin a gasar kofin Afirka da Morocco ke karbar bakunci.

Najeriya, wadda ke rike da kofi uku a jere na 11 jimulla, za ta fafata a wasa na 14 da hukumar kwallon kafar Afirka za ta gudanar.

Falcons tana rukuni na uku da ya hada da Afirka ta Kudu da Burundi da kuma Botswana da za su kece Stade Moulay, Rabat, Morocco.