Amfanin citta ga lafiyar ɗan'adam

Bayanan bidiyo, Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyon
Amfanin citta ga lafiyar ɗan'adam
An wallafa

Citta wata nau'in saiwa ce da masana suka bayyana cewa ta samo asali ne daga yankin Kudancin Asia, kuma tana daga cikin kayan kamshi da ake amfani da su wajen dafe-dafen abinci ko kuma abin sha.

Ana kuma iya amfani da citta a danyar ta, ko busasshiya ko a garin ta har ma da ruwan ta, kuma tana da saukin samu a kasuwanni a fadin duniya.

Dakta Zarah Zambuk wata likitar jama'a a Najeriya ta kuma ce an shafe fiye da shekara 5000 ana amfani da citta a duniya.