Me ya sa wasu ba sa kuka idan aka yi musu mutuwa?

    • Marubuci, Aisha Salisu Babangida
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Broadcast Journalist
    • Aiko rahoto daga, BBC News, Abuja
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 4

Mutuwa na ɗaya daga cikin abubuwan da suka fi tayar wa ɗan'adam hankali. A mafi yawan lokuta, idan aka sanar da mutum mutuwar wanda yake ƙauna, hakan na dugunzuma musu rai har su fashe da kuka.

Wannan wata hanya ce a al'adance da ɗan'adam kan yi amfani da ita wajen bayyana halin da yake ciki ba tare da amfani da bakinsa wajen furtawa ba.

Amma ba kowa ne hakan ke faruwa da shi ba. Akwai mutanen da idan aka yi musu mutuwa, ba sa zubar da hawaye nan take. Wasu ma kan kasance suna rarrashin sauran ƴan'uwa, suna gudanar da shirye-shiryen jana'iza, har mutane su fara tambayar ko ba su ji zafin rashin ba.

Kasancewar a al'adance ana tsammanin mutum zai yi kuka idan aka yi masa mutuwa, wasu na ganin cewa idan ba ka yi ba, tamkar mutuwar ba ta maka zafi ba ne ko kuma kana da taurin zuciya.

Me ke hana mutum kuka?

Amma rashin kuka nan take yana nufin mutum ba ya jin zafin mutuwa? Ko kuwa akwai wani abu bayan hakan?

Rashin yin kuka ba ya nufin rashin baƙin ciki ko damuwa, kamar yadda wani masanin ilimin halayyar ɗan'adam, Dr. Musa Ibrahim ya bayyana wa BBC.

Masanin ya ce rashin yin kuka nan take bayan mutuwar masoyi ko wani ɗan'uwa abu ne da ake yawan gani, kuma ba alamar cewa mutum ba ya ƙaunar mamacin bane.

Ga wasu daga cikin dalilan da masanin ya lissafo:

Kwakwalwa na shiga yanayin gigicewa (Shock)

A farkon jin labarin mutuwa, kwakwalwa kan shiga wani yanayi daake kira shock. Wannan na iya sa mutum ya kasa yin kuka ko ma ya kasa yarda da abin da ya faru.

Rashin yarda da abin da ya faru (Denial)

Wasu ba sa yarda cewa da gaske mutumin ya mutu ko kuma suna jiran a ce kuskure ne. Wannan na iya hana hawaye zuba nan take.

Nauyin alhakin da ke kansu

Idan mutum yana da wasu nauyin da ya kamata ya ɗauka nan take, kamar kula da yara, shirya jana'iza ko taimaka wa iyali, ba laile kuka ya zo masa ba, zai iya danne zuciyarsa har sai daga baya.

Kowa na nuna jimami da baƙin ciki ta hanyarsa

Masana sun ce ba kuka kaɗai ne alamar baƙin ciki ba. Wasu shiru ne, wasu su ware kansu, wasu kuma su ci gaba da gudanar da ayyukansu duk da zafin da suke ji a zuciya.

Tarbiyya da al'ada

A wasu gidaje ko al'ummomi, ana koya wa mutane kada su nuna rauni ta hanyar kuka, musamman maza. Wannan na iya sa mutum ya danne kukansa ko ya kasa yin sa a bainar jama'a.

Hawaye na iya zuwa daga baya

Masanin ya bayyana cewa wasu mutane ba sa kuka a ranar mutuwar, amma bayan kwanaki, makonni ko ma watanni ne baƙin cikin ke bayyana sosai.

Masanin ya ce rashin kuka ba yana nufin mutum bai damu da mamacin ba ko bai ƙaunace shi ba. Yadda mutum ke fuskantar baƙin ciki yana da alaƙa da halayensa da yanayin da yake ciki da kuma yadda kwakwalwarsa ke sarrafa damuwa.

'Na rasa mahaifi ne kwanaki biyu bayan na haihu'

Irin wannan yanayi ya faru da ni a lokacin da na rasa mahaifina kwanaki biyu kacal bayan na haihu.

Saboda ciwon jiki da gajiyar haihuwa, ban ma iya yin kuka ba, abin ya dinga min kamar mafarki.

Ƙanina ne ya kira ya faɗa min rasuwarsa, ina kwance ina jinya, har ma da baƙi a lokacin su zo suna min murnar haihuwa. Na ɗauki kusan minti biyar ina ƙoƙarin fahimtar labarin, sannan na sanar da maigidana mutuwar sai na ce masu mu tafi mu gansa kafin a yi masa sutura.

Da muka isa gida, mutane sun cika, motar ɗaukar gawa ta iso, ƙannena suna cikin tashin hankali, wasu ma suna ta suma. Ni da babbar yayata ba mu samu damar nuna baƙin ciki ba, domin mu ne manya, sai muka riƙa ƙarfafa sauran iyali, muna ansan ta'aziyya.

Sai bayan kusan makonni uku ne, ina zaune ni kaɗai, na tuna da shi, har na kira lambarsa. Da na ji ta yi ringing amma ba a ɗauka ba, sai na fashe da kuka. Tun daga lokacin, duk lokacin da na tuna da shi ko kewarsa, ba na iya riƙe hawayena.

'Na yi wata guda ina ganin kamar mafarki nake yi'

Shi ma Malam Sani Abdullahi, ma'aikacin gwamnati mai shekara 42 a Kano, ya ce ya kasa kuka ba lokacin da ya rasa mahaifiyarsa.

"Da aka kira ni aka ce mahaifiyata ta rasu, ban yarda ba. Na isa gida, na ga mutane suna kuka, amma ni ban iya zubar da hawaye ba. Na shiga shirya jana'iza, ina karɓar masu ta'aziyya, ina kula da ƙannena yara da ƴan uwa na."

Ya ce mutane da dama sun yi mamakin yadda bai yi kuka ba.

"Wasu ma suna cewa wai ba ni da zuciyata mai laushi. Amma ni a raina na san ba haka ba ne. Ina jin zafin rasuwar sosai, amma ban san yadda zan bayyana shi ba."

A cewarsa, bayan kusan wata guda yana cikin mota yana komawa gida daga aiki, sai ya ji wata wa'azi game da darajar iyaye, nan take ya fashe da kuka.

Wasu ma ba sa kuka kwata-kwata

Musa Ibrahim ya jaddada cewa babu wata hanya guda da ta dace wajen jimamin mutuwa.

Wasu hawaye kan zubo musu nan take, wasu kuma sai bayan wani lokaci. Wasu ma ba sa kukan kwata-kwata.

"Abin da ya fi muhimmanci shi ne a bai wa mutum damar jimamin mutuwar da aka yi masa yadda zuciyarsa ta karɓa, ba tare da masa hukunci ba."

Domin a ƙarshe, ba saurin kuka ba ne ke nuna girman soyayya. Wani lokaci, waɗanda ba sa kukan ma ya kamata a damu da su saboda su ne ke haɗiye abubuwa ba tare da bayyanasu ba, wanda shi ne ke iya janyo wata matsala ta lafiya.

"Kuma zuciya na iya ɗaukar lokaci kafin ta amince da gaskiyar cewa wanda take ƙauna ya tafi har abada." masanin ya ƙara da cewa.

Yaushe ya kamata a nemi taimako?

Masanin ya ce idan mutum ya shafe watanni yana cikin matsanancin baƙin ciki da ke hana shi cin abinci ko bacci ko aiki ko kula da iyalansa, ko kuma yana jin rayuwa ba ta da amfani, yana da kyau ya nemi taimakon ƙwararren masanin lafiyar kwakwalwa.