Tsananin zafin rana da iska sun ƙara rura gobarar daji a kudancin Turai
Tsananin zafin rana da ya kai kusan digiri 40 a ma’aunin Celsius tare da iska mai ƙarfi sun ƙara rura gobarar daji a sassan kudancin Turai, inda dubban jami’an kashe gobara ke ci gaba da kokarin dakile yaɗuwarta.
Gobarar ta riga ta ƙone kusan murabba’in kilomita 200 na filayen dazuka da ciyayi a ƙasashen Portugal, Spain, Girka da Faransa, lamarin da ya tilasta hukumomi ɗaukar matakan gaggawa domin kare rayuka da dukiyoyi.
A yankin gabashin tsaunukan Pyrenees da ke Faransa, inda gobarar ke ci gaba da yaɗuwa, hukumomi sun haramta wa masu kallo tsayawa a kan hanyar gasar tseren keke ta Tour de France, wadda matakinta na uku zai ƙare a yankin ranar Litinin.
A Girka kuwa, gobarar daji ta lalata masana’antu biyu da ke kusa da birnin Thessaloniki.
A arewacin Portugal kuma, jami’ai sun ce an samu gagarumar nasara wajen shawo kan wata babbar gobara da ta tashi a yankin. rewrite this and make the story tally with the heasdline Tsananin zafin rana da iska sun ƙara rura gobarar daji a kudancin Turai.